1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun sojojin Senegal sun shiga cikin Gambiya.

Salissou Boukari
January 19, 2017

Sojin Senegal sun shiga Gambiya bayan da a yammacin wannan Alhamis 19 ga watan Janairu na 2017, aka rantsar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasar Gambiya.

Sabon shugaban kasar Gambiya Adama Barrow yayin rantsuwar kama aiki a Senegal
Sabon shugaban kasar Gambiya Adama Barrow yayin rantsuwar kama aiki a SenegalHoto: picture-alliance/AP Photo

 

Rundunar sojojin Senegal ta ce dakarunta sun shiga cikin kasar Gambiya a wani mataki na taimakawa Adama barrow wanda aka rantsar a matsayin sabon shugaban kasar. Rikicin siyasa ba ta kare ba a kasa matukar Yahya Jammeh bai sauka daga karagar mulki ba.

Wani babban hafsan sojin Senela din kanar Abdou Ndiaye a wani gajeren sako da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar da cewa sun shiga cikin kasar ta Gambiya.

Tun da farko Adama Barrow ya yi rantsuwar kama aiki a birnin Dakar na Senegal.

Sanye cikin fararan kaya a gaban iyalansa da sauran wakilan kasashe da kuma na kungiyar ECOWAS, sabon shugaban kasar ta Gamabiya Adama Barrow ya yi rantsuwar kama aiki a Dakar babban birnin kasar Senegal. Cikin jawabinsa na farko, Shugaba Barrow ya mika godiyarsa ga shugaban kasar Senegal da ya bashi damar zama a kasarsa tare da tawagarsa har ya zuwa wannan lokaci, sannan ya jinjina wa shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari da kuma tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama kan irin kokarin da suke yi na ganin komai ya yi dai-dai a Gambiya. Sabon shugaban ya sha alwashin zama shugaban dukkanin al'ummar kasarsa.

Shugabanci ga duka al'umma

Ofishin jakadancin Gambiya a Snegal, inda Baroow ya yi rantsuwar kama aikiHoto: Reuters/E. Farge

Ya ce:"A yau al'ummar Gambiya da dama sun hada kansu da nufin ba wa kasarsu sabuwar makoma. Daga wannan rana ni ne shugaban kasar Gambiya ko da kun zabeni ko kuma akasin haka, za ku iya zama daga cikin masu gina kasarmu da aka gina kan shugabanci na gari da bin dokokin kasa da kare hakkin dan Adam da kuma girmama 'yancin al'umma. Gwamnatina za ta gudanar da muhimman gyare-gyare da suka hadar da gyaran kasa da kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa, da nufin bunkasa dimokaradiyyarmu."

Tun dai a ranar 15 ga watan nan na Janairu ne shugaban mai jiran gado da wasu na kusa da shi suka isa birnin Dakar, inda suka ci gaba da zama har ya zuwa wannan lokaci da aka rantsar da shi. Kasar Gambiya dai na da tsarin zabe da ya sha ban-ban da na sauran kasashen Afirka. Tsarin da a cewar Ahmed Dieme daraktan cibiyar dabarun sadarwa na yankin Sahel baya bukatar kashe kudi mai yawa sannan kuma mai haske ta yanda ba za a samu magudin zabe ba.Ya kara da cewa wannan matsala ta kasar Gambiya batu ne na shari'a ta bayan zabe wadda kotun tsarin mulkin kasar ba ta warware ba.

Rawar da ECOWAS ya kamata ta taka

John Mahama da Ellen Johnson Sirleaf da Muhammadu Buhari da kuma Macky Sall na tattauna batun GambiyaHoto: Getty Images/AFP/S. Aghaeze

"A cikin tsarin shari'a karar da Jammeh ya shigar abu ne da za a iya karba. Idan har aka dubi batun hukumar zabe da ta sanar cewa akwai kuskure kan adadin da ta bayar na farko, in har kuwa akwai kuskure kenan Jammeh ya na da gaskiya ya shigar da kara, ganin yadda yawan kuri'un da ke tsakaninsa da abokin hamayyarsa ya ragu sosai. Idan har ya kasance kotun kolin kasar Gambiya ba ta da isassun alkalai, kamata ya yi kungiyar ECOWAS ta bayar da alkalai isassu domin su duba wannan kara."

An dai samu makamanciyar wannan takadamma ta bayan zabe a kasar Cote d'Ivoir a shekara ta 2010 da kuma Madagaska, inda shugabannin da suka fadi a zabe suka yi kokarin makalewa akan mulki amma kuma ba su ci nasarar yin hakan ba. A halin yanzu dai sojojin kasashe da dama na yammacin Afirka cikinsu har da na Senegal mai makwabtaka da ita da na Najeriya da ke a matsayin uwa kuma jagora a Afirka, sun kasance cikin shirin ko ta kwana yayin da kasar Ghana ita ma ta bada amannar tura nata sojojin idan har akwai bukata. A yammacin wannan rana ta 19 ga watan Janairu na 2017 din ne kuma, ake sa ran Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan daftarin dokar da kasar Senegal ta gabatar domin ba wa Barrow cikakken iko na yin amfani da sojojin kasa da kasa a kasar ta Gambiya idan har bukatar hakan ta taso.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani