Dakarun Ukraine sun zafafa kai wa Rasha hare-hare
March 16, 2024Yayin da aka shiga kwana na biyu na zaben shugaban kasa a Rasha, dakarun Kiev sun zafafa kai hare-hare a yankunan Rasha masu iyaka da Ukraine inda suka halaka mutane biyu a baya-bayan nan, lamarin da kai shugaba Putin ga sha alwashin daukar fansa.
Harin karshe shine wanda aka kai a Belgorod birni mafi kusa da Ukraine inda aka cilla rokoki guda takwas, lamarin da ya ajalin wata mata da wani mutum tare kuma da jikkata wadansu mutanen biyu kamar yadda gwamnan yakin Viatcheslav Gladkov ya sanar a shafinsa na Telegram.
Sakamakon karuwar hare-haren gwamnan ya kuma sanar da daukar matakin rufe cibiyoyin kasuwanci na birnin da makarantun wasu gundumomi da ke yanki na tsawon kwanaki biyu.
Rahotanni da ke fitowa kuma daga sauran yankunan Rashar na cewa an kama mutane da dama a jiya Juma'a da laifin kawo cikas da zaben shugaban kasar da za a kamalla a gobe wanda zai bai wa shugaba Putin sabon wa'adin mulki na shekaru shida.