1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun wanzar da zaman lafiya ba za su fice daga Lebanon ba

Binta Aliyu Zurmi
October 5, 2024

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke Lebanon sun ce ba za su bar yankin da suke tsugunne a kudancin kasar ba kamar yadda sojojin Isra'ila suka bukata.

Libanon Jisr al-Khardali | UN Fahrzeuge patrouillieren im Süden des Libanon
Hoto: Rabih Daher/AFP/Getty Images

Tawagar ta yi kira ga kasashen Lebanon da kuma Isra'ila da su mutunta kudirin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 a aikace a matsayin mafita daya tilo da za a mayar da zaman lafiya a yankin.

Kudirin na kwamitin sulhu da ya kawo karshen yakin shekarar 2006 da aka gwabza a tsakanin Isra'ila da Hizbollah ya amince da cewar sojojin Lebanon da dakarun wanzar da zaman lafiya ne kadai aka amince su kasance a kudancin Lebanon.

To sai dai tun a farkon wannan makon sojojin Isra'ila suke kokarin kutsa kai ya zuwa yankuna da dama a kudancikn kasar ta Lebanon.