Dakatar da bada tallafi ga Ruwanda
November 30, 2012Talla
Sakatariyar cigaban ƙasa da ƙasa ta Burtaniya Justine Greening ce ta ambata hakan inda ta ƙara da cewar a wannan karon ko kusa London ba za ta aikewa da mahukuntan Kigali fam miliyan 21 da ta saba aike mata ba saboda alaƙarsu da M23 domin a cewar Uwargida Gereenings ɗin wani mataki ne na saɓa alƙawarin da ƙasashen biyu su ka yi.
Wannan matsayi da London ɗin ta ɗauka dai wani yunƙuri ne na matsawa Ruwanda lamba da ta tashi tsaye wajen kashe wutar rikicin na Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo to sai dai Ruwandan ta sha musanta wannan zargi da ake mata na agazawa 'yan tawayen.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman