1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Turai na dakatar da ba da mafaka wa 'yan Siriya

Abdourahamane Hassane
December 11, 2024

Kasashen Birtaniya da Italiya sun dakatar da ayyukansu na neman mafaka na wani dan lokaci ga mutanen kasar Siriya bisa la'akari da halin da ake ciki a kasar.

Hoto: Dilara Senkaya/REUTERS

A baya dai kasashen Sweden, da  Norway da Denmark sun sanar da cewa za su dakatar da aikin samar da mafakar. A Jamus  ofishin kula da ƙaura da kuma 'yan gudun hijira ya dakatar da duk wasu shawarwari kan neman mafaka daga 'yan kasar ta Siriya. A daren Lahadi ne 'yan tawaye karkashin kungiyar masu kishin Islama Haiat Tahrir al-Sham (HTS) suka mamaye birnin Damascus na kasar Syria, inda suka kawo karshen mulkin  Bashar al-Assad.