Dakatar da tattara kudin yaki da Corona a Kamaru
April 30, 2020Talla
Gwamnatin ta bayyana shirin da kasancewa haramtacce tare kuma da bai wa kamfanonin salula guda biyu na Orange Cameroun da na MTN Cameroun wadanda ke aikin tattarar kudin da su rufe asusun ajiyar kudin wanda aka bude a karkashin shirin domin ajiyar kudaden taimakon.
A watan Aprilun da ya gabata ne dai madugun 'yan adawar kasar ta Kamaru ya kaddamar da wannan shiri nasa na neman tallafi kudi a ciki da wajen kasar ta Kamaru domin gudanar da ayyukan yaki da annobar Coronavirus a kasar inda kawo yanzu cutar ta harbi mutun dubu daya da 830 ta kuma halaka 61 daga cikinsu.