A kan matsin lambar Kungiyar EU a rufe babbar hanyar dake shiga libiya daga Nijar wadda ke kan kaida wadda ake yin bincike. Amma duk da haka yan cirani da kasahen yankin yammacin Afirka na ci gaba da kewaye hanyar don shiga Libiya. Kuma masu fasa kobrin kan daukar muguwar hanya mai cike da hadari tare da 'yan ci ranin.