Dala miliyan dubu 16 ta bace a NNPC
March 15, 2016 A wani rahoton da ya mikawa majalisar tarayyar Najeriya dai Mr Samuel Ukura babban mai binciken kudin gwamnatin kasar yace lalle kamfanin na NNPC na da abun amsawa kan yadda tsabar kudin suka kai ga batan dabo a karkashin idon tsohuwar ministar kudin kasar Diezeni Allison Madueke a shekara ta 2014. Wannan dai shi ne zargin da tsohon gwamnan CBN Sanusi Lamido Sanusi ya yi cewa ba za to kimanin dalar Amirka biliyan 16 sun bace daga kamfanin manfetur na NNPC, sai dai wannan zargin shi ne ya yi sanadin koran Sanusi daga mukamin nasa a lokacin.
Kudaden cinikin iskar gas din kasar ta Najeriya dai alal misali a fadar Ukura sun tafi ne zuwa ga wani aljihu na daban, maimakon asusun tarayya na kasar, banda kuma wakaci ka tashi da aka yi da cinikin hajar ta mai da suka karkace zuwa wasu aljihu, sannan kuma kamfanin da ma ministar suka ce karya ne.
Sabon rahoton Ukura dai na dada tabbatar da girman badakalar da ta abku a masana'antar man kasar ta Najeriya, mai tasiri da kuma ake ta'allakawa da kokari na yakin neman zaben da ya shude. Majiyoyi dai sun ce da dama a kudin sun tafi ne a aljihu na masu siyasa da nufin yin kamfen din neman zarcewar shugaba Goodluck Jonathan a zaben bara, kamfen din kuma da ya kare ba sa'a , sannan kuma ya bar baya da muguwar kura. Alhaji Umaru Dembo dai na zaman tsohon ministan mai a cikin kasar ta Najeriya, kuma da ya ce girman satar lallai ta yi kama da kokari na sakaya masu siyasa maimakon sata, domin azurta kai a bangare na jami'ai na tsohuwa ta gwamnatin.
Tuni dai sabuwar gwamnatin 'yan sauyin ta kaddamar da bincike kan yadda aka kai ga wakaci ka tashi da dubban miliyoyin nairori na kudin, daga asusu daban-daban na kamfanin NNPC. Kuma sannu a hankali ana kara kiran sunayen masu siyasar tare da dangantasu da irin wadanan kudade da suka ce sun amsa domin yakin neman zaben, amma kuma dawan ya yi dameji a bangaren 'yar lemar. To sai dai kuma girman adadin da ya kai kusan rabin kasafin da shugaban kasar mai ci yanzu ya ware domin shirin gyara ga kasar a bana, ya kara tada hankula cikin kasar da ke kallon ta yi baki ta yi muni a batar da wadannan kudade a shekara guda.
Dr Hussaini Tukur Hassan, dai na zaman wani masani ga harkokin mulki da siyasa na kasar, kuma a fadarsa an wuce gona da iri da suna na siyasar da tasirinta ke tsaka ta kwakwalwa ta 'yan kasar a halin yanzu. Ana dai saran majalisun kasar biyu za su yi nazari a bisa rahoton kafin daga baya a mika shi ga shugaban kasar domin daukan mataki.
Yawan kudin da aka ce sun bace dai kai rabin daukacin kasafin kudin kasar na bana. to sai dai kuma sannu a hankali suna da ma kimar Malam Sanusi Lamido Sanusi tsohon gwamnan CBN wanda ya fallasa labarin bacewar kudin, kuma ta kai aka koreshi daga mukaminsa, a yanzu batun na kara tabbata, bayan da babban mai binciken kudi na Tarayyar Najeriya ya fitar da wani rahoton da ya tabbatar da zargin na Sanusi.