1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Daliba ta kashe malamarta da wata daliba da bindiga a Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 17, 2024

Rundunar 'yan sandan Amurka ta ce dalibar da ta yi harbin mai suna Natalie Rupnow, ta mutu bayan harbe kanta da ta yi.

'Dan sandan Amurka
Hoto: Scott Olson/AFP/Getty Images

Wata daliba mai shekaru 15 dauke da bindiga ta harbe malamarta da wata daliba har lahira a Amurka, sannan kuma ta raunata wasu guda shida, bayan bude musu wuta a makarantarsu ta Christian school da ke jihar Wisconsin.

Karin bayani:Trump ya sake tsallake rijiya da baya a yunkurin halaka shi

Rundunar 'yan sandan Amurka ta ce dalibar da ta yi harbin mai suna Natalie Rupnow, ta mutu a lokacin ake kan hanyar kai ta asibiti, sakamakon harbin da ta yi wa kanta da kanta.

Karin bayani:Mai yunkurin halaka Donald Trump ya gurfana a kotu

Tuni dai shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya nuna kaduwarsa da faruwar lamarin, yana mai kiran majalisar dokokin kasar ta hanzarta amincewa da yi wa dokar mallakar bindiga gyara, don dakile yawaitar kisan da ake samu a dalilin hakan.