Hatsarin mota ya kashe dalibai 21 a Uganda
July 17, 2026
Talla
'Yan sanda sun wallafa hotunan motar da ta kife da 'yan makaraantar, tare da bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan ko hatsarin na da wata alaka ta daban. An kuma kai sauran wadanda suka jikkata asibitin gaggawa.
Hatsarin motar bas mai haddasa mutuwa abu ne da ya zama ruwan dare a kasar Uganda sakamakon rashin kyawun titi, a watan Oktoba, motocin bas biyu sun yi taho mu gama a wani babban titin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 46.
Wani rahoto na shekarar 2024 ya nuna cewa an samu hadurran da suka yi sanadiyyar mutuwa har guda 4,434, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5,144.