Najeriya: Dalibai 6 sun mutu a hannun 'yan bindiga
August 24, 2021Talla
Rahotanni daga Najeriya na cewa, dalibai shida sun mutu a hannun 'yan bindigan da suka yi garkuwa da su, suna daga cikin dalibai 136 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su, daga wata makarantar Islamiyya da ke garin Tegina a jahar Neja. Suna daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su tun a watan Mayun wannan shekarar ta 2021.
A wani karin bayani da yayi ma kamfanin dillancin labarai na Reuters, Abubakar Garba Alhasan, wanda shi ne shugaban makarantar da aka sace daliban, ya ce, 'yan bindigan sun sheda masa cewa, yaran sun mutu ne bayan sun sha fama da rashin lafiya. Ya kara da cewa, sun nemi a biya su kudin fansa, don amso sauran daliban da ke hannunsu.