Takarar Bouteflika na fuskantar cikas
March 3, 2019Talla
A cikin fushi daliban dauke da kwalayen rubutu a kantituna su na shewar cewa "Ba mu yadda ba, muna bukatar canji." An tsaurara matakan tsaro a muhimman wurare da ke cikin birnin, yayin da motocin tsaro ke ta sintiri a sassa daban daban domin taka wa masu bore birki wajen hana Shugaba Boutaflika mika takardun takararsa karo na biyar a hukumance.
Shugaba Abdelaziz Boutaflika yana da shekaru 82, ya yi mulkin shekaru 20 amma tun shekarar 2013 rashin lafiyar shanyewar barin jiki ya hanashi fitowa cikin jama'a, abinda wasu 'yan kasar ke ganin ba shi da lafiyar iya shugabanci amma shugaban ya ce a shirye ya ke ya sake wani wa'adin mulki.