1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalibai sun yi zanga zanga kan muhalli

Abdullahi Tanko Bala
March 15, 2019

Dubban 'yan makaranta a fadin duniya sun kaurace wa makarantu a wannan Juma'ar don gudanar da zanga zanga akan tituna domin adawa da gazawar gwamnatoci wajen daukar matakan shawo kan dumamar duniya. 

Fridays for future Schüler Schülerinnen Streik Schulstreik Klima Klimawandel Berlin
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Koall

Zanga zangar ta gama gari ta samo asali ne daga wata daliba 'yar kasar Sweden 'yar shekaru 16 da haihuwa wadda ta rika yin zanga zangar ita kadai a kofar majalisar dokokin Sweden a bara domin jawo hankali mahukunta kan sauyin muhalli. Tun daga wannan lokaci zanga zangar ta rika fadada zuwa sauran sassa na duniya. 


A Jamus dalibai kimanin 10,000 ne suka yi dandazo dauke da kwalaye suna rera take dake cewa daukar matakin kare muhalli ya zama wajibi. Sun kuma yi tattakin har zuwa ofishin shugabar gwamnati Angela Merkel.


Daya daga cikin daliban da suka jagoranci zanga zangar Clara Reemtsma ta yi bayani tana mai cewar,


"Matasa a fadin duniya sun hada kansu domin bukatar a daukin gaggawa kan dumamar yanayi, magana ce ta makomar mu, ko da yake bama ganin illar a yau, amma abu ne wanda babu shakka zai shafi duniya baki daya a saboda haka yake da muhimmanci gare mu matasa manyan gobe mu yi magana mu jawo hankali a dauki mataki."