1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBangladesh

Daliban Bangladesh sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 21, 2024

Boren dai ya janyo mutuwar mutane 114 biyo bayan arangama da 'yan sanda da suka rinka harbinsu da bindigogi, bayan fesa musu hayaki mai sa hawaye

Hoto: Muhib Hasan

Daliban Bangladesh sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga, ta nuna rashin goyon bayansu ga sabon tsarin daukar aiki da gwamnatin kasar ta bijiro da shi, duk kuwa da hukuncin kotun kolin kasar na Lahadin nan da ya soke mafi-akasarin bukatun gwamnatin.

Karin bayani:Mutuwar mutane kusan 100 ta janyo dokar ta baci a Bangladesh

Mai magana da yawun gamayyar kungiyar daliban wanda ya nemi a sakaya sunansa ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP matsayarsu kan batun.

Tun farko dai gwamnatin kasar ta gabatar da sabon tsarin daukar aikin gwamnati ta hanyar fifita iyalan wadanda suka yi gwagwarmayar yakin neman 'yancin kai daga hannun Pakistan a shekarar 1971, da kaso mai tsoka, to amma hukuncin kotun kolin Lahadin nan ya zaftare tsarin zuwa kaso 7 kacal cikin 100, matakin da matasa masu zanga-zangar suka ce bai musu ba, sai dai a bar damar a bude ga ko wane 'dan kasa.

Karin bayani:Ana lissafa kuri'u a zaben Bangladesh

Boren dai ya janyo mutuwar mutane 114 biyo bayan arangama da 'yan sanda da suka rinka harbinsu da bindigogi, bayan fesa musu hayaki mai sa hawaye.

Firaminista Sheikh Hasina ta ba da umarnin katse intanet da na layukan waya, tare da sanya dokar hana fita don dakile fantsamar rikicin.

A gefe guda kuma hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa sun ba da umarnin gurfanar da 'yan kasar Bangladesh da aka kama suna zanga-zanga gaban kotu, bayan da suka janyo hatsaniya tare da barnatar da kadarorin al'umma.

Ofishin mai gabatar da kara na kasar ya ba da umarnin ci gaba da tsare wadanda aka kama, gabanin kammala bincike domin gurfanar da su gaban kotu.

Dokokin Hadaddiyar Daular Larabawa sun yi tanadin haramta jam'iyyun siyasa da kungiyoyin kwadago, kuma yawancin kafafen yada labaran kasar na gwamnati ne.