1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zanga-zangar daliban Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
May 7, 2021

A Jamhuriyar Nijar daliban jami’ar birnin Yamai sun yi zanga-zanga domin nuna bakin ciki kan abin da suka kira rikon sakainar kashi da gwamnatin ta Nijar ke yi ga harkokin ilimi a kasar.

Niger Demonsration für Bildungsreform
Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Matakin farko da daliban suka dauka tun da sanyin safiyar ta yau Juma‘a, shi ne na saka motocinsu na safa-safa domin kange hanya ta gadar farko da ake kira Pont Kenedi inda babu wani abun hawa da zai iya ficewa ta wannan hanya da ta hada birnin Yamai din da gunduma ta biyar ta Yamai inda jami'ar take.

Hakan za a iya cewa wani sabon salo ne daliban suka dauka na maimakon su fito su yi wani dauki ba dadi da jami'an tsaro rufe wannan hanya kadai zai haddasa dagulewar zirga-zirgar ababen hawa a birnin na Yamai, daliban sun kiyaye kona tayoyin kan kwalta inda suka konasu a gefe duk don su janyo hankalin magabata zuwa ga tarin matsalolin da suke fuskanta.

Hoto: picture-alliance/AA/B. Boureima

Tuni dai daga bangaran gamayyar kungiyoyin da ke kare hakkin samun ilimi na COADE ta bakin shugabansu Docta Alhaji Laoual Amadou Roufai suka soki wannan lamari inda suka yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukan matakin samun sulhu tare da daliban domin ci gaban karatu.

Karin Bayani:Nijar:Tsarin inganta ilimin yara mata

A baya dai daliban sun kaurewa azuzuwa har sau biyu, kafin daga bisani su sake ba da wani wa'adi ga hukumomin na Jamhuriyar Nijar kan batun matsalolin nasu, sai dai ganin cewa babu wata sasantawa ta kai ga daliban daukan wannan mataki da suka kira matakin farko na kokowar neman inci Iliyassou Idrissa Idrissa mataimakin magatakardan kungiyar daliban cewa ya yi:

Yanzu abun jira a gani shi ne na matakin da gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar za ta dauka kan wannan bore na daliban jami'ar ta birnin Yamai da suka ce sun shafe watanni shida ba tare da samun kudin alawus ba baya ma ga sauran tarin matsalolin da suke fuskanta, inda a yanzu suka ce sun gaji da dadin bakin 'yan siyasa masu magana babu cikawa.