1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daliban Najeriya a kasashen waje na cikin dimuwa

Nasir Salisu Zango MNA
June 24, 2020

Dubun dubatar daliban Najeriya na gararamba a kasashen duniya a sakamakon gazawar gwamnatin kasar na cika alkwarin dawo da su gida biyo bayan barkewar annobar Corona.

Wasu daliban Najeriya a kasar Kuretiya da suka taba samun matsala da hukumomin kasar
Wasu daliban Najeriya a kasar Kuretiya da suka taba samun matsala da hukumomin kasarHoto: Adi Kebo/zurnal.info

Wannan matsala dai ta shafi dalibai da gwamnatocin jihohi da ta tarayya suka dauki nauyinsu da kuma sauran wadanda suka kai kansu, lamarin da wasu daga daliban ke cewar suna daf da fara fasa kantuna domin samun abin da za su ci.

Hukumomi a Najeriya sun dade suna daukar alkawuran kwaso 'yan kasar da suka makale a kasashen ketare a dalilin annobar Corona, sai dai kuma tsawon lokaci gwamnatocin sun gaza cika alkawarin balle irin wadannan dalibai su san tudun dafawa.

Salim Usman guda ne daga cikin dalibai da ke karatu a tsibirin Cyprus ya ce sama da watanni uku kenan suna zaman kare a karofi ba rini ba matsa, har ma wasu sun fara tunanin kaucewa hanya.

Ita ma wata baiwar Allah mai suna Ummu Muhammad da ta je kasar Misrah domin neman magani ta bayyana mawuyacin hali da suke ciki da kuma yadda kullum ake musu romon baka, amma har yanzu shiru kamar an shuga dusa.

Dalibai a harabar jami'ar jihar Legas da ke Kudu maso yammacin NajeriyaHoto: AFP/Getty Images/S. Heunis

Malam Bappa Ahmed shi ne shugaban kungiyar iyayen yaran da jihar Kano ta dauki nauyin karatunsu a kasashen ketare ya bayyana yadda suke cikin kunci da rashin tabbas a dalilin rashin dawowar daliban gida.

To sai dai kuma a nata bangaren gwamnatin Kano ta ce ta fara daukar adadin daliban domin hada karfi da kanan hukumominsu domin daukar matakin da ya dace.

Zuwa yanzu dai dalibai da sauran 'yan Najeriya da ke kasashen waje na cikin dimuwa da rashin tabbacin ranar da za su koma gida da kuma rashin cika alkawuran da gwamnatin Najeriya ke musu, lamarin da ya zame musu gaba damisa baya sayaki.