1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta leko ta koma ga 'yan Najeriya a Ukraine

Uwais Abubakar Idris AH
March 3, 2022

An samu cikas a aikin fara kwaso ‘yan Najeriya da yaki ya rutsa da su a kasar Ukraine, inda bayan shiryawa aka dakatar da jirgin farko da ya kamata ya taso daga kasar Poland zuwa Abuja.

Hoto: ATTILA KISBENEDEK/AFP/Getty Images

Ta dai leko ne ta koma ga ‘yan Najeriyar da suka hallara a filin jiragen sama na birnin Warsaw na Poland domin fara aikin kwaso su zuwa Najeriyar bayan kwashe kwanaki suna jira na ganin sun kai ga tudun na tsira bayan samun arcewa daga yanayi yaki da ya rutsa da su. Shin me ya faru ne da aka dage batun kwaso su bayan an sa masu raye a faruwar haka ? Ambasada Christian Ugwu shi ne jakadan Najeriya a kasar Poland: Ya ce: 'Hali ne na ‘yan Najeriya sai ka nuna da gaske ka ke kafin ka tattara su a wuri daya musamman matasa da ke nuna yarinta, don koda a nan filin jiragen sama sai da jami’ai suka kama wani saboda ya shiga inda bai dace ba, wadannan ne mtsalolin da muka fusknata, amma ina ba da tabbacin cewar ranar Jumma’ah jirgi zai tashi’’ Tuni wata tawaga da majalisar wakilan Najeriya ta ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta isa kasar Romania domin aikin fara kwaso wasu ‘yan Najeriyar sama da dubu daya da suke a can. Can din ma dai ana ci gaba da shirye shirye ne na fara aikin kwaso ‘yan Najeriyar da ke a kasar ta Romaniya. Bayanan da na samu a filin sauka jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sun tabbatar da cewar akwai jirgin saman kasar Turkiya da zai kwaso wasu ‘yan Najeriya wanda ake sa ran isowarsa a ranar Jumma’a nan. Gwamnatin Najeriyar dai ta amince da kasha sama da dalla miyan 8 don wannan aiki bayan da shugaban kasar ya sanya hannu a kan batu, to sai dai jinkiri ko jan kafa ya sanya nuna damuwa a