Najeriya: Za a yi jarrabawar WAEC
July 29, 2020Gwamnatin Najeriyar da ta sanar da ranar bude makarantun sakandire ta bayar da kai bori ya hau ne bayan kai ruwa rana, da tayar da jijiyar wuya da ma barazana da wasu jihohi shida suka yi, a kan batun bude makarantun domin yin jarabawar kamala sakandiren. Karkashin sabon tsarin, daliban da ke shekarar karshe da wadanda suke shekara ta uku za su koma makarantar daga ranar hudu ga watan Augusta, sannan za su fara jarrabawar WAEC ta kasashen Afrika ta Yamma da za a fara daga ranar 17 ga watan na Augusta.
Mr Chukwuemeka Nwajiuba shi ne karamin minista a ma'aikatar ilimi ta Najeriyar, ya yi karin haske kan yarjejeniyar da aka cimma a kan bude makarantun: "Yarjejeniyar ta kunshi cewa hukumar shirya jarrabawa ta kasashen Afrika ta Yamma da kasashen da ke cikinta, sun amince a fara jarrabawar kamar yadda aka tsara a baya wato ranar 17 ga watan Augusta, sannan Najeriya kuma za ta tsara lokacin da za a yi sauran jarrabawar a cikin kasarta."
Murna da doki dai ya cika iyayen yara da ma daliban da suke kalon bude makarantun a matsayin wata dama gare su a kokari na shata kyakyawar makoma ta faninin iliminsu. Duk da fitar da tsarin da za a bi a makarantun da annobar cutar coronavirus ta sanya aka rufe su a baya, kwararru a fanin ilimi na bayyana damuwa a kan halin da ake ciki, sanin cewa akwai sauran jarrabwa iri daban-daban da ba a ma tsara yadda za a yi su ba, domin kuwa dalibai 'yan aji shida na firamare ba sa cikin wadanda aka tsara yadda za su rubuta tasu jarrabawar ta shiga sakandaren.
A yayinda iyayen yara da dama ke nuna tsoro na rashin samun sakamako mai kyau ga daliban saboda kwan gaba kwan bayan da aka dade ana yi, jami'an kula da lafiya na kara jan kunen ganin an tabbatar da bin ka'idojin da aka gindaya na bayar da tazara da sauran matakan kariya daga cutar ta COVID-19, inda gwamnati ta kara wa'adin tsarin sassauta ka'idojin kariya daga cutar da mako guda a cikin kasar.