1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daliban Nijar za su yi aiki da sabon ministan ilimi

Abdoulaye Mamane Amadou
April 19, 2017

Dalibai da 'yan farar hula na tsokaci game da nada Yahouza Sadissou a matsayin sabon ministan ilimi mai zurfi na Nijar bayan da suka gindaya sharadin korar tsohon minista kafin hawa kan teburin tattaunawa da gwamnati.

Niger Niamey Demonstration für besser Studienbedingungen
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Ko da ya ke garambawul din da shugaban kasa Issoufou Mahamadou ya yi wa gwamnatin kasar bai yi wani tasiri ba ga wasu mukamai masu muhimmanci da wasu ministocin kasar suke rike da su ba, amma ya yi tasiri ga dalibai saboda da daya ne daga cikin sharadin da hadadiyar kungiyar daliban kasar USN ta gindaya kafin shigarta  tattauanawa da gwamnatin kasar don fita daga kangin tabarbarewar karatu da fannin na ilimin makarantun bokon Nijar ya tsunduma a yayin da a ke dab da kawowa karshen shekara.

Dama daliban sun ja daga da cewar duk wata dama ta zama tuburi guda a yi sulhu da gwamnati ba zata samu ba face sai an saki mukarraban kungiyarsu da a ka kame a kaso tare da bude jami'a da kuma kakkabe babbar rigar wanda tuni a ke iya kira a yanzu da tsohon ministan Ilimi mai zurfi Mohamed Ben Omar, lamarin da gwamnatin ta karbin koke-koken na kungiyoyin dalibai.

Malam Hassane Soumana Sambo sakataren kungiyar daliai na USN ya ce "zancen komawa karatu fa sai idan mun zauna tare da gwamnati mun ga inda aka kwana kan yaje-yajen aikin dalibai da kuma hanyar da za'a bi don a shafe mana hawaye."


 ‘Yan fafatukar kare hakkin dan Adam da demokaradiyya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan wannan sabon garambawul na gwamnatin Jamhuriyar Nijar mai nasaba da matsalolin daliban makarantun boko. A cewar Alhaji Salissou Amadou tamkar ba a rabu da Bukar bane kuma an haihi Habu, inda ya ke cewa " Ben din ya na cikin gwamnati, idan har ya zamanto a na wasu abubwan ashe ba a magani kenan akwai matsala, laifi kamata ya yi idan ya hau kan mutun to doka ta hau a kan kowa."

​​Yahouza Sadissou ya ce zai samar da maslaha ga rikicin ilimin NIjarHoto: DW/M. Kanta


Duk da ya ke sun dauki alkawarin komawa kan teburin shawara da gwamnatin Jamhuriyar Nijar karkashin jagorancin Firaminista Birgi Rafini, daliban sun ce ba za su sake komawa karatu ba face an tabbatar da kafa wani kwamitin da zai gudanar da bicike don gano dalilan da suka haddasa hasarar rayuwar dalibi guda da kuma muzguna wa dalibai da dama a ranar zanga- zangar ta 10 ga wannan Afirilun 2017.