1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dalilan Burkina Faso na dakatar da kafafen labarai na ketare

Hairsine Kate Musa Tijjani Ahmad/Mouhamadou Awal
May 8, 2024

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta rungumi salon danne hakkin 'yan jaridu inda ta sallami tashoshin ketare da dama ciki har da DW, a yayin da matakinta na yaki da ta'addanci ke ritsawa da rayukan fararen hula.

'Yan jarida na ketare na maida hankali kan Burkina Faso saboda ayyukan ta'addanci
'Yan jarida na ketare na maida hankali kan Burkina Faso saboda ayyukan ta'addanciHoto: Zoeringer/Imagespic Agency/IMAGO

Kungiyoyin kasa da kasa na kakkausar suka a kan matakin dakile gudanar da aikin jarida ta hanyar tsage gaskiya kan al'amuran da ke faruwa a Burkina Faso da sauran kasashen yankin Sahel. Tun lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a watan Satumban 2022 a birnin Ouagadougou, sojojin suka sanya kafar wanda daya da kafafen yada labarai na ketare bisa zargin rufa-rufa kan batun keta hakkin bil'Adama.

Muheeb Saeed, manajan sashen kula da kare hakkin dan Adam na Gidauniyar Yada Labaran Yammacin Afrika ya ce ai sun san za a rina kasancewar tun lokacin da sojojin Burkina Faso suka hau kan mulki ,suka sanya kafar wanda daya da kafafen yada labaran ketare. 

Wani bango a birnin Ouagadougou, wanda ya ce " Mu yi taka tsantsan kuma mu bada gudunmawa.Hoto: AP/picture alliance

Ya ce: " Muna bibiya tare da tattara rahotannin cin zarafin da Burkina Faso ke yi wa kafafen yada labarai a 'yan shekarun nan, kuma mun yi Allah wadai dangane da abubuwan da suka faru, duk da cewa ba mu yi mamaki ba duba da salon kamun ludayin gwamnati.''

Hatta kafafen yada labaran cikin gida na Burkina Faso ba su tsira ba, inda a bara sojojin suka rufe gidan Radiyon Omega, kafar yada labarai mafi farin jini a kasar, sakamakon gabatar da wani shiri da ya soki sojojin Jamhuriyar Nijar da ke kawance da ta Burkina Faso. 

Karin bayaniBurkina Faso ta sake dakatar da wasu kafafen yada labarai

Masu sharhi kan siyasar Afrika sun ce matakin na Burkina Faso na da nasaba da yunkurin sojojin na murkushe 'yan ta'adda a yankin,  Muheeb Saeed ya ce: " Kafafen yada labaran ketare na da matukar tasiri ta fuskar diflomasiyya dangane da daukar mataki kan wani al'amari. Idan ya kasance hakan to babu shakka dole a kai musu farmaki, a ci zarafinsu, a dakatar da su don isar da sako."

Sojoji sun kai sumame a lokacin da 'yan ta'adda suka addabi al'umma a 2019Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Burkina Faso na son cin karenta ba babbaka dangane da boye wasu bayanai a yunkurinta na murkushe 'yan ta'adda, wanda fargabar abin da ka je yazo ya sanya 'yan jaridan kasar dogara da samun rahotanni da labarai da sojojin ke bukata, a cewar Sadibou Marong da ke zma daraktan kungiyar  'yan jarida nagari na kowa da ke aiki a yammacin Afrika. Ya ce: " A duk lokacin da sojoji za su kai farmaki ga kungiyoyin 'yan ta'adda, ana samun rahotannin keta hakkin bil'Adama kuma ba sa son kafafen yada labarai masu 'yanci  su kwarmata su''.

Karin bayani:'Yan jarida na aiki cikin wahala a Afirka

Tashar DW  ta Jamus da TV5 Monde da Le Monde na Faransa  da The Guardian ta Burtaniya sun fada fushin gwamnatin sojin Burkina Faso, wanda kafin daukar wannan mataki sun dakatar da BBC da Muryar Amurka VOA.