1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaYemen

Dalilan 'yan Houthi na barazana a Bahar Maliya

Kersten Knipp ATB/MAB
December 19, 2023

'Yan tawayen Houthi a Yemen na kai hari da jirage marasa matuka kan jiragen ruwa a tekun Bahar maliya. Suna baranazar kai hari kan dukkan wani jirgin ruwa da ya nufi Israila matukar ba a shigar da abinci a zirin Gaza ba.

Mayakan Houthi sun dade suna fito na fito da gwamnatin Yemen
Mayakan Houthi sun dade suna fito na fito da gwamnatin YemenHoto: Khaled Abdullah/REUTERS

Hare-hare na 'yan Houthi kan manyan jiragen ruwa na kasa da kasa ya yi kamarin da ya sa manyan kamfanonin jiragen ruwa na dakon kaya suka sanar da cewa ba za su sake tura jiragensu bi ta mashigin Bab al-Mandab ba. Dama fai daya ne daga cikin muhimman hanyoyin sufurin jiragen ruwa na duniya da ya hada tekun fasha da Bahar maliya.

Shin su wane ne 'yan Houthi?

'Yan Houthi sun fito ne daga wata kabila daga tsaunukan arewacin Yemen da ke iyaka da Saudiyya. Kungiyar na daya daga cikin 'yan Zaidi na mabiya darikar Shi'a. Sabanin sauran 'yan Shi'a 'yan zaidi ba su yi imani da dawowar Mahadi ba. Sai dai riko da 'yan Houthi suka yi da darikar Shi'a muhimmin jigo ne na kyakkyawar alakarsu da Iran wadda ke kallon kanta a matsayin jagora kuma mai wakiltar muradun 'yan Shi'a a yankin.

'Yan kabilar Zaidi da ke zama kashi 1/3 na jama'ar Yemen na da yawa a kungiyar HouthiHoto: Khaled Abdullah/REUTERS

A Yemen, 'yan Zaidi ne kashi daya cikin kashi uku na jama'ar kasar. Ta fuskar manufa kuwa, 'yan Houthi na nuna tsantsar adawa da Amurka da Israila  tare da yin tofin Allah tsine ga Yahudawa da kuma kiran nasara ga Islama. Wajen akida kuwa, suna aiwatar da tsattsauran dokokin Musulunci a yankunansu a arewacin Yemen. Sun hada gwagwarmayar addini da kin jinin kasashen Yamma da kuma Israila. 

Babbar manufar 'yan Houthi

Tun bayan  juyin  juya hali na kasashen Larabawa a 2011, 'yan Houthi  suke kara zargin gwamnatin tsakiya a Sanaa  da mayar da 'yan Zaidi saniyar ware da ma take hakkokinsu. Suna ma zargin gwamnatin da karkata  ga Israila da Amurka. 'Yan Houthin sun bijire wa gwamnatin Abdu Rabbo Mansour Hadi a 2014. Kawancen sojojin hadaka na kasashen waje da Saudiyya ta jagoranta ya taimaka masa zama a karagar mulki zuwa 2015. Tun daga wannan lokaci kawancen ke yakar 'yan Houthi ba tare da samun nasara ba.

Harkokin kasuwanci na sukurkucewa a tekun Bahar Maliya bayan barazanar 'yan HouthiHoto: Houthi Military Media/REUTERS

Dr Jens Heibach na cibiyar nazarin siyasar kasa da kasa ke Hamburg aJamus GIGA ya yi tsokaci yana mai cewa: " 'Yan Houthi ba wai sun bayyana ba ne tun farkon fara yakin, amma kungiya ce wadda ta samo asali tun shekarun 1990. Ana ma tsammanin cewa kungiyar ta faro tun 1994 lokacin da Hussein Badreddin al Houthi ya kafa ta, dan majalisar dokoki na Yemen wanda ya yi adawa da shugaban kasa na wancan lokaci Ali Abdallah Saleh. Hakikanin abin da 'yan Houthi suke nema abu ne mai sarkakiya a tsawon lokaci. To amma abin da ya faru a 'yan shekarun baya-bayan nan bayan da suka karbi ragamar mulki a arewaci ya fayyace karara."

Kasashen da ke adawa da 'yan Houthi

Saudiyya ta nemi sasantawa da 'yan Houthi bisa jagorancin KuwaitHoto: Almasry Alyoum/dpa/picture alliance

Saudiyya na goyon bayan gwamnati da ke rike da kudancin kasar Yemen yayin da 'yan Houthi ke iko da arewaci da kuma suke samun tallafi daga Iran. Shi ya sa ma ake kallon yakin Yemen a matsayin yakin bayan fage tsakanin Saudiyya da Iran. A kan haka ne Dr Jens Heibach na cibiyar nazarin siyasar kasa da kasa ke Hamburg a Jamus GIGA ya ke cewa: " Kalmar yaki ta bayan fage ba ta kwanta min ba, saboda ta na nuna kamar ka fake ne da wani ko kuma wani tsani a dangantaka tsakanin wanda aka fake da shi da kuma ainihin wadanda ake fadan da su daga waje musamman a kan 'yan Houthi da Iran. Ina dan taka tsan-tsan saboda idan ka tambaye ni ko 'yan Houthi suna samun umarni daga Iran, har yanzu ina dai taka tsan-tsan".

Ana kallon 'yan Houthi a matsayin aminai na kurkusa da gwamnatin Iran. Kuma su kan su 'yan Houthi suna daukar kansu a matsayin 'yan gwagwarmaya da suka ja daga da Israila da Amurka wadanda akidarsu ta zo daya da ta 'yan Hizbullah na Lebanon da kuma kungiyoyin fafutuka da dama a Iraqi da Siriya. Sai dai ba za a iya fayyace irin taimakon da Iran ke bai wa 'yan Houthin ba. Kuma babu tabbas ko Iran ta taka gagarumar rawa a harin da 'yan Houthin ke kai wa a baya bayan nan kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya.