1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da ruruwar rikicin 'yan aware a kamaru

Mouhamadou Awal Balarabe SB
October 11, 2018

Rikicin aware na kasar kamaru na ci gaba da ruruwa sakamakon kafewa kan bakansu da bangarorin ke yi wajen zama kan teburin sulhu. Sai dai masana tarihi da siyasar kasar sun ce sai an magance matsalar tun daga tushe.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Kalubalen aware da Kamaru ke fuskanta ya samo asali ne daga kwaceta daga hannun Jamus da Turawan Faransa da na Ingila suka yi, bayan da suka samu nasara a yakin duniya na daya shekaru 100 da suka gabata. Hasalima yankin da ake kira Kamaru ta Kudu da Ingila ta raina ya taba zama karkashin sa idon Majalisar Dinkin Duniya kafin a shirya zaben raba gardama da ya sa ta hade da yankin Faransanci da ake kira Jamhuriyar Kamaru bisa tsarin Tarayya a ranar daya ga watan oktoban 1961. sai dai daga bisani shugaban kasa na wancan lokaci Ahmadu Ahidjo ya yi misayar yawo da shugabannin bangaren Ingilishi, lamarin da ya sa aka shirya zaben raba gardama a 1972 wanda ya bada damar kafa hadeddiyar Jamhuriyar Kamaru. Amma bayan da Paul Biya ya hau mulki ya canja sunanta zuwa Jamhuriyar kamaru kawai, tare da barin tauraro daya a kan tutar kasar maimakon biyu, Tun wannan lokaci ne 'yan yankin Ingilishi suka fara korafin cewa ana mayar da su saniyar ware. Malamin tarihi na jami'ar Buea Richard Ndifor ya dora alhakin wannan rikici kan bangarori da dama.

Hoto: DW/F. Muvunyi

"Majalisar Dinkin Duniya da ke da alhakin tabbatar da cewa Birtaniya ta mutunta yarjejeniyar kai wa ga yancin kai da aka cimma na da laifi. shi ma Shugaban kasa na wancan lokacin Ahmadu Ahidjo na da nashi laifin saboda ya take yarjejeniyar da aka cimma a 1961. Shi ma shugaba na yanzu Paul Biya na da nashi laifin saboda lokacin da ya hau mulki ya canza sunan kasa daga hadeddiyar Jamhuryair kamaru zuwa Jamhuriyar kamaru."

Hoto: DW/F. Muvunyi

Shekaru biyun da suka gabata ne 'yan yankin Ingilishi suka tashi haikan wajen kwato hakkinsu, inda suka fara gudanar da zanga-zanga domin neman gwamnati ta mutunta kundin tsarin mulki, wanda ya tanadi yin daidai wa daidai tsakanin Faransanci da Ingilishi. Amma kin yin hakan da ta yi da wadannan butuwa ya sa 'yan aware neman raba kasar gida biyu idan ba a koma kan tsarin Tarayya ba. Achille Mbembe, malamin jami'a kuma mai sharhin kan al'amuran yau da kullum a Kamaru ya ce ba abin maimaki ba ne kasancewa gwamntin Biya na amfani da kabilanci wajen raba kawunan 'yan kasa.

"Saboda wannan gwamnati ta dogara ne a kan matsanacin kabilanci. Ba a fuskanci irin wannan matsala a Kamaru a cikin shekarun 1960 zuwa farkon shekarun 80 ba. Akwai alamar hadin kan kasa a wancan lokaci. A gaskiya, batun kabilanci ba ya kasancewa a cikin harkokin siyasa. Wannan gwamnati ce ta bude babin kabilanci a tsarin siyasar kasar, wanda za a iya magance shi ne kawai ta hanyar sakar wa yakunan marar gudanar da al'amuran yau da kullum, ko ta hanyar komawa kan tsari na Tarayya."

Hoto: Getty Images/AFP

Ita gwamnatin paul biya ta yi tsayuwar gwamin jaki kan wannan batu, inda ta ce ba za ta taba tattaunawa da masu raba kamaru gida biyu ba, yayin da su kuma 'yan aware suka ce ba wanda zai hanasu ballewa domin kafa kasa ta kansu mai suna Ambazoniya ba. Sai dai Richard Ndifor ya ce sulhu ne kawai mafita kamar yadda cocin katolika ta kudirin aniyar shiryawa.