Taron masu lalurar gani a Damagaram
November 11, 2025
Taron masu lalurar ganin na bana ya gudana ne, a daidai lokacin da galibin al'ummar kasashen nahiyar ke cikin yanayi na tabarbarewar tsaro. Sarkin makafin Damagaram Lawali Bahago ne, ya kasance mai masaukin baki. Bayan adu'o'i da wasanin kade-kade da bushe-bushe, sun kuma mika gaisuwa ga mai alfarma sultan na Damagaram kamar yadda suka saba. A yanzu dai magabatan kasashen sun dauki matakin tafiya tare da masu lalurar ganin da ma sauran masu bukata ta musamman, a kokarinsu na ganin an gudu tare an kuma tsira tare.
Daga cikin mahalarta taro, har da sarkin makafin Sokoto da ke Tarayyar Najeriya Mahamadu Haruna. Gwamnan jahar Damagaram Kanal Sani Masallaci cewa ya yi: "Shugaban kasa Janar Abdourahamane Tiani da kuma duka manyan kasar nan sun ce in zo in mika gaisuwarsu.......Ba za ku sake ganin wani mai lalurar gani yana roko ko yana bara ba, za a sa niyya a gani ....a kawo musu agaji in ya so su samu abun yi........"