Dambarwa kan rabon riga-kafin cutar corona
October 21, 2021Hukumar Lafiya ta Duniya tayi kira ga manyan kasashen duniya da suka yi alkwarin yin raba daidai na allurar riga-kafin corona da kasashe matalauta, da su gaggauta cika alkawuran da suka dauka don ceto rayukan jama'a. Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus yayi wannan kiran ne, a gabanin taron koli na kasashen mafi karfin tattalin arziki a duniya da zai gudana a mako mai zuwa.
A yayin da kasashen da aka tsara bai wa tallafin allurar ke fuskantar karanci, bayan da suka karbi kashi arba'in cikin dari da suke bukata, kasashen yamma nada allurar kimanin miliyan dari biyu da arba'in da suka adana, ba tare da an yi amfani da su ba, lamarin da Gordon Brown, wani jakadan hukumar ya kira da abin kunya.
Wannan dai, ba shi bane karon farko da ake yin kira ga manyan kasashen na duniya, kan su tausaya don ganin sun wadata kasashe masu bukatar allurar riga-kafin corona, cutar da ta hallaka sama da mutum miliyan daya da rabi a sassan duniya tun bayan bullarta a Disambar 2019.