Karin haske kan takunkumin kan China
May 29, 2018Talla
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren cinikin Amirka Wilbur Ross ke dab da kai ziyara kasar ta China don bude wata sabuwar tattaunawar kan hanyoyin warware rikicin cinikayyar da ya balle tsakanin kasashen biyu bayan China ta fara yi wa Amirka barazanar sanya takunkumi a kan dukkan kayan da aka shigo dasu daga kasar. Da ta ke karin haske hukumar ciniki ta kasar China ta shawarci kasar ta Amirka da ta mutunta sharadan da kasashen biyu suka amince tun da farko.