Dambarwar shugabanci a kasar Libya
February 11, 2022
Sabon Firaministan wanda majalisar wakilai da ke da mazauni a gabashin Libya zai shugabanci gwamnatin hadin kan kasa kamar yadda kakakin majalisar Abdullah Bliheg ya tabbatar.
Bayan da Fathi Bashaga ya samu amincewar illahirin membobin majalisar da aka yi zama da su da kuma janye takarar kujerar firaministan da Khalidul Baibas ya yi. Daga wannan rana Bashaga shine halastaccen firaministan Libiya da zai maye gurbin Dbaibah wanda wa'adin mulkinsa ya kare tun ranar 24 ga watan Disambar 2021.
Tuni dai wasu ke daukar matakin a wani sabon yunkurin janar Haftar na kwace ikon birnin Tripoli da dabara, bayan da ya kasa kwace shi da karfin soji, yadda aka jiyo kakakin rundunar sojin da ke masa biyayya, Ahmad Mismari na cewa:
Rundunar sojin Libiya na sanar da cikakken goyan bayanta ga matakin majalisa na nada Fathi Bashaga a matsayin firaminista. A kuma shirye rundunarmu take ta bashi duk kariyar da ta wajaba don kai Libiya ga mafificin yanayi.
Wannan matakin dai ya kara ta da kurar dambaruwar siyasa a kasar, dama fargabar komawa ruwa a yakin basasar da aka yi nasarar kashe wutarsa da kyar da gumun goshi a bara.
A nasa bangaren, firaminista mai ci, Abdulhameed Dbaibah wanda a ranar alhamis ya tsallake rijiya ta baya, bayan da wasu da ba a san ko su wanene ba suka bude wa motarsa wuta ya sha alawashin ci gaba da rike iko har sai ya danka shi ga zababbiyar gwamnatin da za a zaba watanni 14 da ke tafe kamar yadda majalisar dokoki da ta dattawan kasar suka ayyana.
Ita ma dai majalisar dattaijan kasar da ke da helkwatarta a birnin Tripoli ta siffanta nada sabon firaiministan da wani riga malam masallaci da makwadaita mulki karfi da yaji ke yi.
Kamar yadda itama Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa a wurinta har yanzu, Dbaibah ne halastaccen shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar, tana mai kira ga bangarorin siyasar kasar da su ci gaba da tattaunawa da juna don warware sabanin dake tsakaninsu.
Hakan dai ya jefa talakawan Libiya cikin yanayin gaba Kura baya Siyaki inji Dr Nizar Hikmah wani mai sharhi kan lamuran siyasar kasar:
A yanzu Majalisar dokoki na son sai ta kwace iko da matsayin firaiminista. Ita kuma ta Dattawa na son ganin an yi raba gardama kan kundin tsarin mulki. A yayin da tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar ke son ganin an yi zaben shugaban kasa ko ta halin kaka. Shi kuma talakan Libiya shi ake ta tambola da shi.