1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dambarwar siyasa a majalisar dokokin Ghana

October 22, 2024

Bangaren gwamnati wacce ta koma adawa bayan ballewar wasu wakilanta daga jam'iyya ta hau kujerar naki akan karbar sabon matsayin su a majalisar dokokin kasar Ghana

Ghana Wahlen I John Dramani Mahama  und Mahamudu Bawumia
Hoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images, Olympia de Maismont/AFP

Kafin wannan takkadamar dai, dukannin bangarorin na da kujeru 137, har sai da wani dan bangaren gwamnati wanda ya dawo majalisa a matsayin dan takara mai zaman kansa ya sake kulla alaka da bangaren gwamnati, abinda ya tilasta marasa rinjaye da ya koma da rinjayen a yanzu amincewa da matsayin. Babbar tambayar ita ce ko anyi bi doka da oda? Dr Tony Aidoo, datijon kasa kana tsohon ministan tsaro ya yi tsokaci

Yace abin kunya ne a ce akwai wani yunkuri daga majalisar zartaswa da bangaren shari'a na lalata tsarin shugabancin kasa a bisa kauce wa kundin tsarin mulki, domin kundin tsarin mulki da tanade-tanadensa bai kirkiri wani gibin wani gyara ba a kotun koli. Ayyukan majalisa da suka sabawa kundin tsarin mulki, su ne kotun kolin kasa ke da hurumin zartas da fassara bama hukunci ba.

Hoto: Cristina Aledhuela/AFP

Makasudin wannan cece-kucen wanda ba farko kenan ba da ake fuskanta, kuma ko shin takkadamar ta majalisar dokoki irin wannan musamman akan maganar shigowar sojjoji a majalisar dokokin, wani gwaji ne akan dokokin kundin tsarin mulkin Ghana? Masanin kimiyyar siyasa Dr Richard Amoako Baah ya yi bayani.

Yace da farko dai zan fara ne da cewa akwai tarin kurakurai a yadda aka rubuta kundin tsarin mulkin kasar Ghana, kuma a hakan za'a iya cewa babu wanda ya tafka kuskure. Shi ya sa muka fada wannan tsaka mai wuya, domin babu wata dokar da ta hana wa kowane dan kasa canja ra'ayinsa, dan shi ta yaya ne idan wani dan takarar shugabanci ya tsaya a zaman kansa ba shi wannan yancin, kowa idan ka shiga wata jam'iyya ba za ka iya sauya sheka ba? Me yasa? domin kowane bangare zai kasance ne ya aiwatar da hukunci a bisa huruminsa da yancinsa

Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

An dai sami rudani a cikin majalisar inda dukannin bangarorin suka cakudu, a bangaren masu rinjayen a cewar ta hannun daman kakakin majalisar, kana daga bisani marasa rinjaye a yanzu NPP suka fice wanda ya janyo rera wakoki daga bangaren NDC. Jim kadan bayan ficewar dai shugaban marasa rinjayen Afenyo markins ya gana da manema labarai.

Yace al'adar mu al'ada ce ta kiyaye doka, ta kan kotu ne magabatan mu ke daidaita kuskure tun daga shekarar 1992 wajen kare zaman lafiyar nan da muke mora. A yanzu da ya iso kan mu, ba zamu ba da wata dama a cikin rashin tsari da NDC ke nema ba, ba zamu yi wannan wasan kwaikwayon da su ba na yunkurin gurbata dimukradiyya da lalata kasa ba. Mun fahimci cewa da siyasa, amma kamata ya yi mu yi ta da tsarin la'akari da jama'a. Dama dai hukuncin kotun akan majalisa ce da kakaki ba wani dan majalisa ba, kuma hukunci ya isa ga kakaki dan shi dole mu tsaya a nan kuma mu girmama hukuncinsa tun da ya kasance a dimukradiyyarmu tun daga 1992, dan haka na yi amannar cewa koda baya ra'ayin hukuncin kotun koli, ya san na yi.

Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Duk da kauracewar dai majalisa ta ci gaba da sabgoginta ba tare da tangarda ba, bayan da kakakin ya bai wa mutum hudun damar ci gaba da ayyukansu na mazabu har a jira hukuncin kotu na karshe.

Yanzu haka bangaren NDC na da wakilcin mutum 136 a yayin da NPP ke da wakilcin mutum 135. Sai dai zaman jiran yadda za ta kaya nan da kwanakin da ke tafe, musamman la'akari da kasafin gwamnati na rubu'in farkon sabon shekara, a watannin Oktoba da Nuwamban mai kamawa ya kamata su kasance a gaban majalisa dan sahalewa.