1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasa wajen rajistar sabuwar jam'iyya a Najeriya

March 11, 2013

Sabuwar jam'iyyar APC ta fara samun ƙalubale tun a matakin yin rajista, inda tuni ta zargi jam'iyyar PDP mai mulki da ƙoƙarin yi mata zagon ƙasa

Attahiru Jega, Independent National Electoral Commission Chairman, declares Nigeria's incumbent President Goodluck Jonathan as the winner of last Saturday's presidential election, in Abuja, Nigeria, Monday, April 18, 2011. Jonathan clinched the oil-rich country's presidential election Monday, as rioting by opposition protesters in the Muslim north highlighted the religious and ethnic differences still dividing Africa's most populous nation. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Shugaban hukumar zabe INEC Attahiru JegaHoto: AP

Ƙasa da makkoni uku da kafa sabuwar jam'iyyar adawa ta APC a tarrayar Najeriya, sabon rikici na neman kunno kai a tsakanin jamiyyar da tace jam'iyyar PDP mai mulkin ƙasar na kokarin yi mata zagon ƙasa ga neman rijistar a hannun hukumar zaben kasar ta INEC.

Ta dai fito da ƙarfi irin na ban mamaki. Ta kuma kai ga girgiza shugabanni dama talakawan cikin jamiyyar PDP mai mulki, to sai dai kuma tana shirin fuskantar kalubalanta na farko ga jam'iyyar adawa ta APC da yanzu haka ke fuskantar barazanar rasa samun rijistar sa cikin
kasar.

Jam'iyyu daban-daban sunaye kusan iri guda
Tuni dai aka kai ga samun jam'iyyun masu taken APC guda biyu da yanzu haka kuma takardun su na neman rijistar ke gaban hukumar zaben ƙasar ta INEC a wani abun dake zaman ba sabun ba kuma ya fara tada jijiyar wuya cikin kasar.

Duk da cewar dai gamin gambizar adawar ya kai ga haihuwar All Progressive Congress kwanaki huɗu bayan nan dai wasu da suka boye launi da kallarsu dai sun fito da Africa People Congress da suka ce suna bukatar hukumar zaben kasar ta INEC tayi wsa rijistar taka rawa cikin harkokin siyasar kasar.

Abun kuma da ya tada hankali tare da fara nuna yatsa a tsakanin 'ya'yan jamiyyar dake zargin hannun PDP a cikin yunkurin, da a cewar Senator Lawalli Shuaibu dake zaman sakataren jam'iyyar can dake zaman daya daga cikin gamin gambizar jam'iyyun ya fada

Gwagwarmayar demokraɗiyya a Najeriya
Tashin hankali ko kuma gwagwarmaya a kokarin tabbatar da demokaradiya dai daga dukkan alamu dai fagen siyasar kasar ta Najeriya na shirin fuskantar gwagwarmayar da tuni ta fara nuna alamun baki da duhu ga yan adawar kasar.

Ko bayan zargin amfani da hukumomin tsaron ƙasar wajen binciken
gwamnonin dake gaba cikin sabon tsarin na APC dai ko a karshen mako wani jigon sabuwar jam'iyyar ya fuskanci fushin yan sanda a garin Kaduna bayan da yayi gargaɗin fito na fito dama kila tashin hankali shigen na ƙasashen Larabawa in har akayi watsi da bukatar samun rijistar tasu.

Senator Sani Ahmed Yarima dai ya share tsawon awoyi yana yiwa yan sandan kasar jawabin me ka sani abun dake nuna alamun fa da jan aiki ga yan adawar da ke tunanin karba a wajen PDP a cikin sauki. To sai dai kuma a cewar Hon Bala Bawa Ka'oje dake zaman ma'ajin jam'iyyar PDP na ƙasa dai duk wani ƙoƙari na ta'allaka PDP da halin da yan jamiyyar APC ke fuskanta to zargi ne da bashi da tushe kuma ke zaman karatun tsoro.

Abun jira a gani dai na zaman iyakar rikicin da haɗewarsa da matsalar tsaron kasar ta nigeria ke iya kaiwa ga barazana ga daukacin demokaraɗiyar da ƙasar ke taƙama a kanta.

Hoto: AP
Hoto: DW/U. Musa

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi