1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da cece-kucen siyasa a Nijar

Larwana Malam HamiMarch 6, 2015

Masu fashin baki kan al'amuran siyasa a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da yin hannunka mai sanda ga 'yan siyasar kasar domin ganin suna aiki da tsarin dimokaradiyya.

Shugaba Mahamadou Issufou na NijarHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

Kiran dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da talakawa da kungiyoyin matasa da ke kiran kansu 'yan kishin kasa ke ci gaba da maida martani game da dambarwar siyasar kasar. Daga batun cin hanci da karbar rashawa zuwa rashin iya jagoranci da ma take dokoki na daga cikin irin abubuwan da 'yan adawar kasar ke zargin masu mulkin da aikatawa da kuma ci gaba da yin cece-kuce biyo bayan hukuncin da wata kotun Faransa ta ba da game da sayen jirgin shugaban kasa.

Zauren majalisar dokokin Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

A cewar Mahaman Mutari na jam'iyyar ARDR babu gudu babu ja da baya kan zargin da sukewa gwamnatin na cin hanci da karbar rashwa. To amma ga Sani Sabo kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya jam'iyyyun adawar basu da bakin cewa wani abu dangane da batun na cin hanci da karbar rashawar.

Rashin kishin kasa daga 'yan siyasa

A hannu guda kuma kungiyoyin matasa da ke kiran kansu da 'yan kishin kasa a Jamhuriyar ta Nijar na ci gaba da fassara baki dayan 'yan siyasar kasar da marasa kishin kasa. Adam Mustafa jagoran kungiyar MJR ta matasa na daga cikin masu irin wana ra'ayi, inda ya ce sun dade da gano cewa su kansu 'yan adawar ma suna yi ne domin kwadayin mulki kawai. A wurare mazaunar jama'a dai daga inuwar safe zuwa ta maraice batun cece-kucen 'yan siyasar ne abun tattaunawa ga talakawa.

Zanga-zanga a Nijar Domin adawa da Boko HaramHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Kouam

Bukatar aiki da doka da oda


To ko yaya masana siyasa ke hangen makomar siyasar kasar a irin wanan hali na kwan gaba kwan baya? Abdu Maman Sanussi masani ne a kan al'amuran siyasa, ya kuma ce dole ne sai an yi amfani da doka da oda sannan mulkin dimokaradiyya ya dore. Kawo yanzu dai talakawa sun kama hanyar dawowa daga rakiyar 'yan siyasar Jamhuriyar ta Nijar inda masu akidar sai Mahadi ka ture ke ci gaba da shafa nasu kalangun da suke ganin cikin kitson da wuya a samu kwalkwata.