Burkina ta yi sabon shugaba
February 16, 2022Talla
A wani biki ta gidan talabijin na kasar ne dai, Damiba ya sha rantsuwar kama ragamar mulki tare da alkawarin kare martaba da darajawa kundin tsarin mulkin Burkina Faso.
An gayyaci 'yan jaridar cikin gida kalilan banda na ketare, a bukin da ya gudana a wani karamin daki a bainar wakilan majalisar tsarin mulkin kasar, majalisar da ta tabbatar da shi a matsayin shugaban kasa ahukumance a makon da ya gabata.
A ranar 24 ga watan Janairun ne dai Damiba, mai shekaru 41 da haihuwa ya jagoranci kifar da mulkin shugaba Kabore, biyo bayan fushin al'ummar kasar ta hanyar yin zanga zanga, kan yadda tsohon shugaban ke wa harkar tsaro rikon sakainar kashi, da ya jagoranci asarar rayuka.