Cikin damuwa na ruwan sama kamar da bakin kwarya da sauro mai haddasa cuta, mazauna garin Rann ke fadi tashin rayuwa, duk da cewa sojojin Najeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram. 'Yan bindigar sun lalata makarantu da turakun layukan waya. Hatta a asibiti rayuwa ta yi kunci.