1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa kan sabbin hare hare a Hormuz

Abdullahi Tanko Bala
July 10, 2026

Wasu jerin hare hare ta sama da ba a san daga inda aka harbo b, sun fada Iran bayan Amurka ta sanar da kawo karshen hare harenta

Hare hare kan Iran
Hare hare kan IranHoto: AFP

Hare haren da suka faru a ranar Alhamis a daidai lokacin da Iran ke shirin binne gawar marigayi jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei sun fada wasu yankuna a kudancin Iran.

Kasar dai ba ta dora laifi akan kowa ba tukuna ko da yake wani dan majalisar dokoki ya gargadi kasar hadaddiyar daular Larabawa kan goyon bayan da ta ke bai wa Amurka a yakin da ta ke yi da Iran.

Amurka ta dage cewa dole ne a bude mashigin ruwan Hormuz ba tare da karbar haraji daga jirage ba.

Sai dai Iran ta ce mashigin wanda kaso daya cikin biyar na jiragen ruwa da ke dauke da mai da iskar gas suke wucewa, ta cikinsa dole ne ya ci gaba da zama karkashin ikonta, kuma wajibi ne duk jirgin da zai ratsa mashigin ya biya haraji ga Tehran, duk da a baya an shafe gomman shekaru kasashen duniya na daukar mashigin a matsayin hanyar ruwa na kasa da kasa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW