SiyasaMexiko
Dan bindiga ya bude wuta a filin wasan kwallon kafa a Mexico
January 26, 2026
Talla
Magajin Garin birnin Salamanca, Cesar Prieto, ya ce 'dan bindigar ya isa filin jim kadan bayan kammala wasan sada zumunci tsakanin matasa. Prieto ya ce lamarin na daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta a Mexico, inda ya bukaci Shugaba Claudia Sheinbaum da ta yi duk mai yiwuwa wajen murkushe ayyukan 'yan bindiga a kasar.
Karin bayani:Mutum bakwai sun halaka a hadarin jirgin sama a Mexico
Mexico na daya daga cikin kasashen da ke fama da ayyukan kungiyoyin 'yan daba da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi. Hukumomin Mexico sun ce an samu raguwar kashe-kashen mutane a 2025, idan aka kwatanta da 2016, wanda kashi 17.5 bisa 100 ke mutuwa a duk mutum 100,000.