Dan bingiga ya kashe mutane a Amirka
November 20, 2018Talla
Magajin garin birnin na Chicago da kuma ofishin hukumar 'yan sanda, sun ce daya daga cikin wadanta suka mutun wata mata ce da ke aiki a asibitin na Mercy Hospital da abin ya faru.
Shi ma dan bindigar ya mutu, sai dai ba a tabbatar da ko ya mutu ne sakamakon musayar wutar da suka yi da jami'an 'yan sanda ko kuma kashe kanshi ya yi da kanshi ba. Shi dai dan bindigar sai da ya auni wajen da mutane ke masu yawa kafin ya buda wutar.
Lamarin kuwa kamar yadda bayanai ke nunawa ya samo asali ne daga wata 'yar hatsaniya da ta kaure a wajen ajiye motoci na asibitin.