Dan Iran ya ci nasara
May 2, 2012A bayan nazari da muhawara mai tsanani, yanzu dai an zabi wadanda suka sami nasarar cin kyautar rubuce-rubuce na Blogs na DW a bana. Wata tawaga ta alkalan kasa da kasa ta zabi rubuce rubucen Blogs da suka fi daukar hankali da kuma shafunan yana-gizo da suka fi bada sha'awa a fannoni dabam dabam har guda shidda a gasar ta wannan shekara.
Alkalan sun zabi rubuce-rubucen Blog na wani dan Persia, mai suna Arash Sigarchi a matsayin mafi ma'ana da daukar hankali a wannan shekara. Shafin sa da ya sanyawa suna wai Window of Anguish, marubucin na Blog yakan gabatar da rahotanni game da keta hakkin yan Adam da kuma sauran al'amuran da suka shafi matsayin rayuwa da halin zaman jama'a a kasar sa ta haihuwa wato Iran. Sigarchi tun shekara ta 2008 yake zaune a Washington a Amirka a matsayin dan gudun hijira. Alkalan suka ce sun zabi shafin sa na Blog ne saboda marubucin ba ma yana da kafofi ne a ciki da wajen Iran na samun labaran sa ba, amma daga cikin duka wadanda suka shiga takarar shine yafi hanyoyi na samun bayanai.
Shi kuwa barubucin Blog dan kasar Mali, Boukary Konate, shine ya sami kyauta ta musamman a fannin al'adu da ilmantarwa. Alkalan da suka zabe shi, sun yaba da ganin cewar Boukary burinsa shine ya wayar da kan al'ummar Mali a game da muhimmancin amfani da yanar-gizo, wato Internet. Tun shekara ta 2008 yake rubuce-rubucen sa karkashin sunan Fasokan cikin harsunan Bambara da Faransanci.
Kyautar DW ta Blog a bangaren gwagwarmayar kare hakkin yan Adam an bayar da ita ne ga wani shafi dake gwagwarmayar kare hakkin jama'a da neman a saki Razan Ghazzawi. Shafin na Facebook, an bude shi ne bayan da hukumomin Syria suka tsare wata mai rubude-rubuce na Blog mai suna Razan Ghazzawi a watan Disamba na bara. Ko da shike daga baya an sake ta, amma an sake kama ta a watan Fabrairu na wannan shekara, amma aka sake ta daga baya. Tun bayan wannan lokaci, shafin na Facebook, wadanda suka bude shi suka ce sun sadaukar da aiyukan sa ga sauran marubuta Blog dake tsare.
Sauran fannoni da alkalan na rubuce-rubucen Blog tda DW ta shirya a bana, da suka sami kyautuka, sun hada harda tashar Video da tafi daukar hankali, inda aka bada kyautar ga wani mai shirya Video na China Pi San da kyautar kungiyar yan jaridu ta duniya da aka baiwa wata yar jarida mai suna Abu Sufian yar Bangladesh da rubutun Blog na shafi Jamusanci da yafi ban sha'awa da aka bada kyautar ga shafi Jules Blog, wanda ya kunshi labarin wata budurwa da ta zama gurguzuwa sakamakon hadari, kuma tayi amfani da shafin na Blog domin sanarwa duniya labarin rayuwar ta.