1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salah Khashoggi yabar Saudiyya

Abdul-raheem Hassan
October 25, 2018

Salah Khashoggi babban dan Jamal Khashoggi ya tafi Amirka tare da iyalansa, bayan da masarautar Saudiyya ta amince da hujjojin da aka gabatar kan kashe mahaifinsa.

Saudi Arabien - Sohn von vermisstem Journalisten Khashoggi bei König Salman
Hoto: picture-alliance/dpa

A karon farko Saudiyya ta amince da hujjojin Turkiyya na cewa an dade da shirya kisan fitaccen dan jaridar da ke rubuta wa jaridar Washington Post. Kamfanin dillancin labaru na Saudiyya ya ruwaito babban mai shigar da kara na Saudiyya bin Abdalla na cewa wadanda suka kashe dan jarida Jamal sun aikata kisan da gangan, duk da cewa Saudiyyan ta yi ta fitar da bayanai masu karo da juna kan kisan.

Saudiyya na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga manyan kasashen duniya kan bayyana hakikanin gaskiyar abinda ya faru da dan jaridar bayan da aka gayyace shi zuwa ofishin jakadancinta da ke Turkiyya ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2018. 

Shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana kisan a matsayin rufa-rufa mafi muni a tarihi.