Dan kunar bakin wake ya kashe jami'an Pakistan 15
July 24, 2026
Rundunar Sojin Pakistan ta ce wani dan kunar bakin wake da ya samu rakiyar wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani shingen binciken jami'an tsaro a Arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro 15.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a, ta ce jami’an tsaro sun dakile harin da aka kai da daddare a garin Tank da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa, inda suka kashe mayaka 12.
Harin bam ya kashe mutane da dama a Pakistan
Sojojin sun zargi kungiyar Tehrik-e-Taliban Pakistan wadda aka fi sani da Taliban ta Pakistan, da kai harin.
Ko da yake TTP ba daya ba ce da Taliban da ke mulki a Afghanistan amma kungiyoyin biyu na da alaka da juna.
Pakistan ta dade tana zargin gwamnatin Taliban ta Afghanistan da bai wa mayakan TTP mafaka, zargin da gwamnatin Kabul ke ci gaba da musantawa.
Pakistan ta mika wa Amurka martanin yaki kan Iran
Ya zuwa yanzu dai kungiyar TTP ba ta ce komai ba kan zargin.