Dan majalisar Najeriya na shan sukar aurar da 'yan mata 100
May 17, 2024Kakakin majalisar Abdulmalik Sarkindaji, ya kekesa-kasa kan cewa ya yi hakan ne domin ya taimaki al'ummar da yake wakilta, domin su ci gaba da gudanar da kyakkyawar rayuwa, matakin da ministar al'amuran matan Najeriyar Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi kakkausar martani kan matakin inda take cewa an tilasta musu kuma wasu basu kai munzalin yin aure ba.
Karin bayani: Sojojin Najeriya sun zubar wa mata 10,000 juna biyu
Ba sabon al'amari bane gangamin aurar da mata a lokaci guda a tarayyar Najeriya musamman a shiyyar arewacin kasar, inda ko a watan Janairun wannan shekara dan majalisar dokokin kasar daga jihar Borno Muktar Aliyu Betara, ya aurar da mata 180 da Boko Haram suka hallaka iyayensu.
Karin bayani: Nijar: Damuwa kan yawan mutuwar aure
Kazalika a shekarar da ta gabata gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta aurar da mata 1,800 a wani shiri da ta yi wa lakabi da auren-gata.