Dan makaranta ya daba wa mutane 25 wuka a China
November 16, 2024Wani matashi dan shekara 21 ya halaka mutane takwas tare da raunata 17 a birnin Wuxi dake gabashin kasar China da yammacin Asabar a cewar sanarwar 'yansanda.
Lamarin ya faru ne kwanaki kalilan bayan wani direba ya murkushe mutane 35 har lahira baya ga wasu 43 da suka samu raunuka a wata farfajiyar wasanni a birnin Zhuhai da ke kudancin kasar ta China.
China ta daure mutum 15 bayan ruftawar wani gini
'Yansanda sun bayyana cewa matashin tsohon dalibi ne da ya kamata ya kammala karatunsa a wannan shekarar ta 2024 amma ya fadi jarrabawa.
Yansandan sun kara da cewa ya koma makarantar ce saboda ya nuna bacin ransa ta hanyar kashe mutane kamar yadda ya tabbatgar musu.
Matakin Amurka na cefanar wa Taiwan makamai ya bakanta ran China
Mahukuntan sun kara da cewa ana can ana aikin gaggawa na jinyar wadanda suka samu raunuka a birnin Yixing.