Dan Masar ya lashe lambar yabo ta Bobs 2014
May 10, 2014An yaba wa Mosa'ab Elshamy bisa gagarumin aiki daga titunan birnin Alkahira.
Ya dogara a kan kyamararsa ko da a cikin mawuyacin hali ne na tashe-tashen hankula a kan titunan Alkahira ko wajen daukar hoton zanga-zangar mutane da ke cikin bacin rai, a kullum mai daukar hoton na kasar Masar Mosa'ab Elshamy yana kusa da wurin da abubuwa ke faruwa. Matashin dan shekaru 23 dai yana karatun fasahar alkinta magunguna ne lokacin da gwamnatin Hosni Mubarak ta fadi. A lokacin daukar hoto na zama abin sha'awa ne gare shi.
Amma wannan ya canja lokacin juyin juya halin da aka samu a Masar, sannan Elshamy ya gane irin karfin tasiri da hotuna ka iya samu lokacin wani rikici. A hira da DW ta hanyar sadarwar Skype cewa ya yi: "Dole na fita. Na ga hakan a matsayin nauyi a kai na na daukar wadannan hotuna, kuma na gane cewa mutane na sha'awar ganin hotunan."
Ya yi watsi da karatun jami'a ya mayar da hankali kan aikin jarida na daukar hoto. ba da jima wa ba hotunansa suka fara bayyana cikin kafafan yada labaru na kasa da kasa ciki har da mujallu irinsu "Time Magazine," da "Paris Match," da "The New York Times" da kuma "Rolling Stone." Ya kuma yi aiki da da manyan kamfanonin daukar hotuna ga jaridu sannan an buga hotunan aikinsa a shafukan farko na manyan jaridu da mujallu a fadin duniya.
Hotunan da 'yan jarida ba su tace su ba
Elshamy na wallafa hotuna a shafukan sadarwa na Twitter, Facebook, Flickr da kuma a shafinsa na yanar gizo. A wannan shafi Elshamy ke ba da labarinsa a cikin hotuna. Batutuwan kuwa sun hada da juyin juya hali a Masar, rashin adalci da kuma zaman alhini. Hotunansa na kuma bayani game da rayuwar yau da kullum na mutanen da yake haduwa da su: yara a cikin raha suna shan ice-cream a shafe a fuska, mutane na shanya a kan rufin gidaje da kuma wasu hotunan da wadanda aka daukar ba su san an dauke su ba.
Ana ganin kusancinsa da mutane a da yawa daga cikin hotunansa. Yana kawo yanayi mai sosai rai da mutane ke ciki kuma ya gabatar da su kai tsaye ba tare da an yi musu gyara ba. Wadannan hotuna suna da wahalar dauka, inji Elshamy. "Abu na karshe da mutane ke son gani a irin wadannan lokuta ita ce kyamera. Saboda haka a dole na koyi yadda zan tinkari mutanen da zan dauka ba tare da na bata musu rai ba."
A tsakiyar boren da ya girgiza birnin Alkahira bayan juyin juya hali, Elshamy ya ce ya zama dole ya yi takatsantsan, wani lokaci ma ba ya son a ganshi, ya kara da cewa yana cikin hadari a duk lokaci da ya daga kyamararsa yana son ya dauki hoto. Hotunansa na nuna abi da ba a zata ba: wani mutum na tsaye cikin gungun mutane da suka fusata jim kadan kafin a harbeshi, da lokutan da iyaye ke dauke da gawarwakin 'ya'yansu a hannunsu, da lokutan da maza da mata ke kuka cikin wani yanayi na rudani. Wadannan su ne abubuwan da Elshamy ya shaida kuma ya nuna wa duniya.
Hotuna suna bayanin kansu
Karfin hotunan Elshamy ya burge alkalai na marubutan The Bobs. Tarek Amr wanda ya zabi Elshamy ga lambar yabon Deutsche Welle ga masu fafatukar ta intanet, ya ce: "Wannan dan Blog yana ba da labarin abubuwa ta wata hanya da ma samu daga sauran kafafan yada labaru. Yana nuna bangarorin rayuwa a masar da ba a gani a duniya saboda abubuwa masu yawa na faruwa a wuraren da ke da wahalar shiga."
Daya daga cikin alkalan Blog Renate Avila ta ce ta gamsu da yadda Elshamy ke iya ba da labari da hotunan da yake dauka.
"Akwai harsuna 14 da suka shiga gasar The Bobs, amma Mosa'ab ba ya bukatar wani yare. Ko da yake ba mu duka muke jin larabci ba, amma dukkanmu mun fahimci karfin tasirin hotunansa," inji ta.
Wannan dai ya gamsar da alkalan 15. Saboda haka suka zabi hotunan blog na Mosa'ab Elshamy a matsayin Blog mafi kyau kuma suka ba shi babbar lambar yabo ta Bobs karo na 10. Wannan wata girmamawa ce ta musamman ga matashin mai daukar hoto: "Tun wasu shekaru da suka gabata The Bobs na nuna irin abubuwan da mutane ke yi a bayan fage. Saboda haka nake farin ciki da wannan karamcin da alkalan suka nuna wa aikina." A gareshi wannan lambar yabo za ta kara karfafa masa guiwa na ci gaba da gudanar da wannan aiki.
Mawallafa: Silke Wünsch / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu