1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dan Najeriya ya kafa tarihin mafi dadewa yana dara

April 20, 2024

Tunde Onakoya ya kafa tarihin ne bayan ya kwashe sa'o'i 58 ya na buga wasan dara ba gajiyawa.

Tunde Onakoya, dan Najeriyar da ya kafa tarihin mafi dadewa ya na buga wasan dara a duniya.
Tunde Onakoya, dan Najeriyar da ya kafa tarihin mafi dadewa ya na buga wasan dara a duniya.Hoto: Yuki Iwamura/AP Photo/picture alliance

Wani dan Najeriya mazaunin Amirka, Tunde Onakoya ya kafa tarihin mafi dadewa yana buga wasan dara a duniya. Onakoya mai shekaru 29 ya kwashe sa'o'i 58 ne ya na buga wasan a dandalin Time Square da ke birnin New York na kasar Amirka da nufin tara dala miliyan daya domin taimaka wa yara marasa galihu a Afirka.

Tun dai a ranar Larabar da ta gabata ce dan Najeriyar da ya kware a wasan dara  ya fara wasan babu gajiya wa har zuwa daren jiya juma'a.

Onakoya ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP irin murnan ya ke ciki sakamakon yadda mutane daga sassa daban-daban suka je nuna masa goyon baya.

A baya dai wanda yafi dade wa yana buga wasan ya kwashe sa'o'i 56 ne. Tuni dai Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya Onakoya murna.