Wani ya kai hari da babbar mota a Jamus
October 8, 2019Talla
Jami'an tsaro a yankin Limburg sun tabbatar da cewa maharin dan asalin kasar Siriya ne da ke neman mafaka a Jamus, sai dai hukumomi na ci gaba da binciken musabbin harin ko yana da alaka da ta'addanci. A shekarar 2016 ma wani dan gudun hijirar kasar Tunisiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu 70 yayin da ya bi ta kan mutane da babbar mota a kasuwar kirsimeti a Berlin fadar gwamnatin Jamus.