1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan takaran gwamnati ya lashe zabe a Jamhuriyar Benin

April 14, 2026

Romuald Wadagni ya lashe zaben shugaban kasa a Benin, inda zai gaji Shugaba Patrice Talon. Nasarar ta zo ne bayan yabo kan jagorantar tattalin arziki duk da matsalolin tsaro a arewacin kasar.

Cotonou 2026: Dan takarar shugaban kasa Romuald Wadagni lokacin gangamin yakin neman zabe
Cotonou 2026: Dan takarar shugaban kasa Romuald Wadagni lokacin gangamin yakin neman zabeHoto: Abadjaye Justin Sodogandji/AP Photo/picture alliance

An bayyana ministan kudi na Jamhuriyar Benin, Romuald Wadagni, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da da aka yi a karshen mako, inda ya samu kashi 94 cikin 100 na kuri'un da aka lasafta.

Hukumar zabe ta ce an samu sakamakon ne bayan kidayar sama da kashi 90 na kuri'un, yayin da dan takarar adawa Paul Hounkpe ya amince da kayen da ya sha.

Wadagni zai gaji Shugaba Patrice Talon wanda ke kammala wa'adinsa, bayan ya samu yabo kan jagorantar tattalin arzikin kasar cikin shekaru goma da suka gabata.

Sai dai duk da hakan, Jamhuriyar ta Benin na fuskantar matsalolin tsaro a yankin arewacinta sakamakon ayyukan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke da alaka da al Qaeda da ma IS.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW