1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Adabi

An bai wa Gurnah na Tanzaniya kyautar Nobel

Abdul-raheem Hassan ZMA
October 7, 2021

Abdulrazak Gurnah marubuci daga kasar Tanzaniya ya lashe kyautar Nobel ta marubutan adabi na wannan shekara ta 2021.

Abdulrazak Gurnah | Gewinner Literaturnobelpreis 2021
Hoto: Simon Hollington/UPPA/picture alliance

Dan kasar Tanyaniza Abdulrazak Gurnah ya lashe kyautar lambar yabo ta Nobel kan rubutun adabi, cibiyar kimiyya ta Sweden da ta ba da kambun, ta bayyana Gurnah a matsayin wanda yake da tasiri kan mulkin mallaka da makomar 'yan gudun hijira. Ya kuma koyar a jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya daga shekarar 1980 zuwa 1982.

Wole Soyinka daga Najeriya wanda ya samu Nobel kan adabi a shekarar 1986Hoto: ullstein bild/dpa

Gurnah mai shekaru 73, wanda aka haifa tsibirin Zanzibar na kasar Tanzaniya amma ya karasa girma a Birtaniya a matsayin dan gudun hijira a karshen shekarun 1960, malami ne a jami'ar Kent, ya kuma wallafa littattafai 10, ciki har da barden littafinsa mai taken Paradise wanda ya duba tasirin mulkin mallaka a gabashin Afirka a zamanin yakin duniya na daya.

Tuni mutane a tsibirin na Zanzibar suka fara nuna farin ciki bayan jin labarin cewa Abdulrazak Gurnah daga wannan tsiribi ya samu kyautar ta Noble wadda take daya daga cikin kyautuka masu tasiri a duniya. Marubuta a ciki da wajen nahiyar Afirka na cikin masu mayar da martani da nuna gamsuwa bisa wannan kyauta.

Wannan kyautar 'yan kasashen Yammacin Duniya ne suka fi samun kyautar gwarzon marubucin adabi tun kafa cibiyar shekaru 120 da suka gabata.

Doris Lessing 'yar Zimbabuwe da ta samu Nobel kan adabi a shekara ta 2007Hoto: picture-alliance/ dpa/O. Berg

Kawo yanzu mutane uku ne daga yankin Kudu da Sahara na Afirka suka samu kyautar Nobel kan adabi baya ga Abdulrazak Gurnah da ya samu na shekara ta 2021, akwai Doris Lessing daga Zimbabuwe wadda ta samu a shekara ta 2007, kana akwai Wole Soyinka daga Najeriya wanda ya samu a shekarar 1986.