'Dan wasan Spain Lamine Yamal ya kafa tarihi a gasar Euro
Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
July 10, 2024
Yamal ya zura kwallo a gasar cin kofin kasashen turai Euro, a wasan da kasarsa ta doke Faransa da ci 2-1
Talla
'Dan wasan kasar Spain Lamine Yamal mai shekau 16, ya kafa tarihin zama 'dan wasa mafi karancin shekaru da ya zura kwallo a gasar cin kofin kasashen nahiyar turai Euro, bayan da ya jefa kwallo a wasan da kasarsa ta doke Faransa da ci 2-1, a zagayen dab da na karshe a daren Talata a birnin Munich, wanda ya bai wa Spain din damar zuwa wasan karshe na gasar da ke gudana a Jamus.
Karin bayani:
Filayen da ke daukar bakuncin gasar Euro 2024
A ranar 14 ga Yuni ne ake fara gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Turai. Jamus da ke daukar bakuncin kasashe 23 ta tanadi filayen wasanni goma. Wasan farko zai gudana a Munich yayin da na karshe zai gudana a Berlin.
Hoto: Arno Burgi/picture alliance / dpa
Filin kwallon Berlin - Kujeru 70,033
Filin wasa na Olympiastadion zai dauki bakuncin wasan karshe na kofin Turai a 14 ga Yulin 2024. Sannan za a yi wasannin rukuni guda uku da zagaye na gaba da na kusa da na karshe a Berlin. An gina filin ne don wasannin Olympics na 1936 kuma an sake gyara shi daga 2000 zuwa 2004. Filin da Hertha BSC ke wasa ne kuma yana karbar bakuncin gasar cin kofin Jamus a kai a kai da manyan gasannin motsa jiki.
Hoto: Arno Burgi/picture alliance / dpa
Filin kwallon Munich - Kujeru 66.026
Ana bude gasar kwallon Turai a Munich wata daya kafin a buga wasan karshe a Berlin. Jamus na fafatawa da Scotland inda take fatan samun nasara tun a farkon gasar. Jamus ta cimma irin wannan buri a gasar cin kofin duniya da ta dauki bakunci a shekarar 2006 - kuma a Munich - inda da ci 4-2 ta doke Costa Rica, ciki har da kwallon da darektan gasar cin kofin Turai Philipp Lahm ya fara zurawa.
Hoto: Peter Kneffel/dpa/picture alliance
Filin kwallon Dortmund - Kujeru 61.524
Wasannin rukuni hudu da zagaye na gaba da kuma wasan kusa da na karshe za su gudana a Signal Iduna Park. Idan Jamus ta haye mataki na gaba, a wannan filin kwallo ne za ta yi wasanninta na gaba. Sai dai a wasan kusa da na karshe na cin kofin duniya a 2006, filin wasan da aka gina domin gasar kofin duniya a 1974 bai kawo wa Jamus wata sa'a ba. Italiya ta samu nasara inda mafarkin Jamus ya rushe.
Shi ne daya daga cikin filaye mafi hayaniya kuma mafi yawan raha a gasar Bundesliga. Wai shin haka zai kasance a gasar kwallon kafa ta EURO? Tawagar Jamus na iya ba da gudummawa a lokacin wasan rukuni na biyu da Hungary a Stuttgart a ranar 19 ga Yuni. Haka kuma za a yi karin wasannin rukuni uku da na kusa da kusa da na karshe a Mercedes-Benz Arena inda VfB Stuttgart ke faranta wa magoya baya rai.
Hoto: Michael Weber/Eibner-Pressefoto/picture alliance
Filin kwallon Frankfurt - Kujeru 48.057
Tawagar kwallon kafar Jamus na buga wasan zagayen farko da Switzerland a daf da mita dari da harabar DFB. Baya ga wasan da Jamus za ta yi da Switzerland, 'yan kallo a birnin Frankfurt za su ga wasu wasanni uku na rukuni da kuma na zagaye na gaba. An gina filin wasan mai rufi don gasar cin kofin duniya ta 2006 ta hanyar kwaskware tsohon filin kwallo na Waldstadion.
Hoto: Florian Gaul/greatif/picture alliance
Filin kwallon Leipzig - Kujeru 46.635
An gina sabon filin wasa na Leipzig don gasar cin kofin duniya ta 2006 a tsohon filin wasan Leipzig Central mai kujeru 100,000. Kungiyar da ta fi amfani da filin da kanfanin Red Bull ya mallaka, ita ce RB Leipzig da ke wasa a Bundesliga. Lokacin da aka bude filin wasan a 2004, ba a kai ga kafa kungiyar ba. Amma a gasar cin kofin nahiyar Turai, za a yi wasannin rukuni uku da zagaye na gaba a nan.
Hoto: Jan Woitas/dpa-Zentralbild/dpa/picture alliance
Filin wasa na Hamburg - Kujeru 50.215
An samar da filin wasa na Hamburg daga 1998 zuwa 2000 ta hanyar amfani da wasu dabaru. A tsohon filin wasan Volksparkstadion, an soke dandanlin guje-guje tare da juya filin da digiri 90. Sannan aka samar da wurin zama na 'yan kallo na zamani domin kawata shi. A gasar cin kofin nahiyar Turai, Hamburg za ta marabci wasu sabon shiga Turai kamar Georgia da Turkiyya da Netherlands a wasannin rukuni.
Hoto: Daniel Marr/Sportfoto Zink/picture alliance
Filin wasa na Gelsenkirchen - Kujeru 49.471
VELTINS-Arena inda FC Schalke 04 ke kwallo, ya kasance filin wasa na farko a Jamus da saman ke rufe gaba daya. Domin ya sami isasshen haske, ana fitar da shi waje bayan kammala wasanni (hoto). A lokacin gasar cin kofin nahiyar Turai za a yi wasannin rukuni guda uku da kuma zagaye na gaba a Schalke, ciki har da karon-batta tsakanin tsoffin zakarun duniya wato Spain da Italiya a wasannin rukuni.
Hoto: Neundorf/Kirchner-Media/picture alliance
Filin kwallon Düsseldorf - Kujeru 46.264
Magoya bayan Düsseldorf na sa ido don ganin yadda za ta kaya a zagayen farko inda za a yi wasannin rukuni guda uku da kuma na zagaye na gaba. Watakila a Düsseldorf ne Jamus za ta lashe matakin rukuni don shiga wasan daf da na kusa da na karshe. Za a iya mayar da filin wasan Düsseldorf zuwa wani dandali - kamar yadda ya faru a gasar cin kofin duniya ta hannu a 2024, inda aka samu 'yan kallo 53,586.
Hoto: Marvin Ibo G?ng?r/GES/picture alliance
Filin wasn na Köln - Kujeru 46.922
Filin wasa na 1. FC Köln, an sake gina shi daga 2001 zuwa 2004 a matsayin filin wasa na gasar cin kofin duniya ta 2006. Yana kan tsohon filin kwallon kafa na Müngersdorf da aka gina a shekarar 1920. A gasar kwallon kafa ta EURO, wasanni na rukuni guda hudu da na zagaye na gaba za su gudana a nan. Wasan Scotland da Switzerland da kuma wasan Ingila da Slovenia za su kasance masu daukar hankali.
Hoto: Thomas Robbin/imageBROKER/picture alliance
Hotuna 101 | 10
Tun farko Randal Kolo Muani ne ya fara jefa wa Faransa kwallo, sannan Lamine Yamal farke wa Spain, yayin da daga bisani Dani Olmo ya zura wa Spain din ta biyu, da ta ba ta nasara.