Dangantaka a tsakanin Japan da Ƙasar Sin
December 27, 2007Talla
Faraministan ƙasar Japan Yasuo Fukuda ya isa ƙasar Sin, don fara ziyarar aiki ta tsawon kwanaki huɗu. Kafin wannan ziyara dai, akwai kyakkyawar dangantakar tattalin arziki a tsakanin ƙasashen biyu. Aa sa ran a lokacin wannan ziyara, Faraministan na Japan zai ƙara ƙulla wasu yarjeniyoyi na kasuwanci da ƙasar ta Sin. Batun rikicin iyaka na daga cikin batutuwan da shugabannin ƙasashen biyu zasu tattauna. Ƙasashen na Japan da Sin na ikirarin mallakar yankin take ne, dake gabas da ƙasar Sin. Yankin a cewar rahotanni na ɗauke ne da ɗanyan man gas a cikinsa.