Dangantaka ta yi tsami tsakanin Amirka da Najeriya
December 2, 2014Wannan matsayi da Najeriya din ta dauka ya zo wa mutane da dama da mamaki domin ana masa kallon wata danba ta lalacewar danganta tsakanin Washington da Abuja wanda suka jima suna dasawa har ma Washington din ke taimakwa Abuja din ta fannin bada horon sojinta don yakar masu tada kayar baya.
Alamu na shiga yanayi na takun saka tsakanin kasashen biyu dai ya fara bayyana ne tun lokacin da Amirka ta ce ba za ta sak sayarwa Najeriya makamai da jiragen yaki masu saukar ungulu ba saboda abinda Amirkan ta kira take hakki na bani Adama da sojin kasar ke yi s wuraren da ake yaki da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.
Gwamnatin Najeriya dai ta musanta wannan zargi da Amirka ta yi inda a hannu guda ta ce matsayin da ta dauka wani yunkuri na dagula lamura a yakin da ta yi da ta'addanci da kuma irin fafutukar da ta ke yi wajen ceto 'yan matan Chibok din nan da 'yan Boko Haram suka sace a watannin da suka gabata.
Wannan yanayi da ake ciki dai ya sanya mutane irinsu Dr. Jibrin Ibrahim da ke jagorantar cibiyar raya demokaradiyya da cigaban kasa a Najeriya ganin dacewar ficewar sojan Amirka daga Najeriya din inda ya ce "sun ki sayar mana da makami kuma sun hana wasu su sayar mana. Game da batun 'yan matan nan na Chibok kuwa sun ce in an gaiyyace su za su taimaka amma sai suka kare da leken asiri saboda haka barin su Najeriyar ba shi da laifi tun da basu da amfani a garemu".
Tun kafin a kai ga wannan mataki dai, dama an sha kai ruwa rana tsakanin jakadan Najeriyar da ke birnin Washington da hukumomin kasar ta Amirka da ke zargin juna da kokari na cin amana ta abota. Duk da cewar dai ya zuwa yanzu rikicin na nuna alamar takaita kansa ga batun na tsaro dai, akwai tsoron rikidewarsa zuwa sassan kasar irin lafiya da tattalin arziki dama zamantakewa.