1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Trump da Juncker

Ramatu Garba Baba LMJ
July 27, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka da shugaban Hukumar Tarrayar Turai Jean-Claude Juncker sun cimma yarjejeniya kan batun kudin fito.

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker da shugaban Amirka Donald Trump
Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker da shugaban Amirka Donald TrumpHoto: Reuters/J. Roberts

Mutanen biyu dai sun amince da su janye duk wani haraji daga kayayyakin da kamfanonin cikin gida ke sarrafawa, baya ga haka akwai batun karin kudin fito da Amirka ta aza kan karafa da goran ruwa da suka yi alkawarin daukar matakin warwarewa. Tuni dai manyan abokan huldar kasuwanci na kasashen Turai suka yi ta jinjinawa Jean-Claude Juncker  bisa rawar da ya taka na shawo kan shugaba Donald Trump na Amirka kan janye karin kudin fiton da ya shirya yi, batun da ke zuwa a yayin da ake cike da fargaba kan illar daukar wannan matakin. A ganawar da suka yi da manema labarai bayan zaman, shugaba Trump ya nunar da cewa akwai bukatar su hada kansu wajen shawo kan matsalolin da suke fuskanta tare.

Karfafa huldar kasuwancin Amirka da EU

Daga bisani Shugaba Trump ya koma kan batun dangantakar kasuwanci, a sau da dama a yayin jawabinsa ya jaddada muhimmancin kulla huldar cinikayya a tsakanin Amirka da Tarayyar Turai da ya ce za ta kasance mafi girma a duniya. Batun waken soya da Amirka ke kokarin bunkasa cinikinsa musanman a kasashen Turai bayan tsananta kudin fito da kasar China ta yi biyo bayan  sabani da Amirkan, ya mamaye jawabin nasu, a na shi bangaren shugaban kungiyar Tarayyar Turai Jean Claude Juncker ya jinjinawa shugaba Trump kan hadin kan da ya bayar a kokarin cimma yarjejeniyar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani