1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ko Amurka za ta kware wa Turai baya?

Jens Thurau MAB/LMJ
December 10, 2025

Hukumomin Jamus da 'yan siyasa na kasar sun yi watsi da sabuwar manufar tsaron Amurka, saboda ta yi hannun riga da alkiblar da Turai ta sa a gaba.

Jamus | Friedrich Merz | Amurka | Donald Trump | Alaka | Turai
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Evan Vucci/AFP

Takaici ya fito fili a tsakanin 'yan siyasar Jamus, game da kalaman da Amurka ta furta a kan tsarin tsaro da makomar nahiyar Turai. Da yawa na dasa ayar tambaya kan ko al'adun Turai na fuskantar barazanar bacewa, sakamakon yawan bude kofofinta ga baki 'yan ci rani? Shin kasashen Turai na lalata tsarin dimukuradiyya?  Shin Amurka a karkashin Donald Trump za ta tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasashen Turai, kamar yadda ya fito fili a sabuwar manufar tsaro da Amurka ta gabatar?

Alakar da ke tsakanin Jamus da Amurka

Ita dai gwamnatin tarayya da ke Berlin, na kokarin jaddada alakar da ta rage da muhimmiyar kawarta wato Amurka. Mai magana da yawun gwamnati Sebastian Hille ya yi tir da sukan EU da ake yi, inda ya ce: "Turai da Amurka suna da alaka ta tarihi a fannin tattalin arziki da al'adu, kuma za su ci gaba da kasancewa abokan hulda na kut da kut."

Yabo kan 'yancin fadin albarkacin baki

02:15

This browser does not support the video element.

Amma ya yi watsi da zarge-zargen cewa, Jamus da Turai suna tauye 'yancin fadar albarkacin baki. Sannan ya ce kuskure ne a yi ikirarin cewa, Rasha ba ta kasance barazana ba, saboda ya saba da matsayar kungiyar tsaro ta NATO kuma "Rasha ce ta dawo da yaki, a nahiyar Turai."

Makomar Ukraine

Shi ma dai shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da firaministan Birtaniya Keir Starmer da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun yi amfani da ganawar da suka yi da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy a birnin Landan, wajen tattaunawa kan sabuwar manufar tsaron Amurka, musamman ma dacewar ta da yakin Ukraine. Merz ya ce: "Babu wanda ya kamata ya yi shakkar goyon bayansu ga Ukraine saboda makomarta na da alaka da ta Turai." 

Sai dai a Berlin, ba a yi mamakin sababbin tsare-tsaren Amurka na mu'amala da Turai ba. Wakiliyar DW, Michaela Küfner da ta rufa wa Merz baya a tafiye-tafiye da dama ta ce: "Dimuwa da ta taso game da shirin Trump ga Ukraine mai matakai 28 tana da girma a fadar gwamnati, lamarin da ya sa sabuwar manufar tsaron Amurka ba ta sake jijjiga kowa ba."

Taron Shugaba Donald Trump na Amurka da takwaransa na Ukraine da shugabannin EUHoto: Alexander Drago/REUTERS

An fahimci cewa Turai ba wai kawai za ta daina aiki tare da Amurka a nan gaba ba ne, amma har ma da cewa Washington tana son wargaza EU zuwa kungiyar kasashe masu al'adu da ke kama da juna.

Martani mai karfi ya zo daga bangaren 'yan siyasa a Berlin, ciki har da Norbert Röttgen masanin manufofin harkokin waje a rukunin 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar CDU mai muki. A yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida ya bayyana cewa: "A karon farko tun bayan karshen yakin duniya na biyu, Amurka ba ta goyon bayan Turai kuma ba ta goyon bayan Ukraine."

Makomar alakar Turai da Amurka

Röttgen ya ce wannan dama ce ta karshe ga Turai, saboda "Idan aka gaza amfani da kudin Rasha da aka karbe wajen taimaka wa Ukraine, wannan yana nufin cewar ba mu shirya tsayawa a kan kafafunmu ba, ba mu shirya kare ikonmu ba."

Daidai da 'yan adawa na jam'iyyar The Greens, sun nuna damuwa bayan wallafa manufofin tsaron Amurka. Shugabar jam'iyyar Green Party Franziska Brantner ta shaida wa rukunin jaridun Funke Media cewa, matsayar Amurka na nufin bai kamata Turai ta sake bata lokaci ba. Maimakon haka, dole ne nahiyar ta zuba makudan kudi don tsayawa a kafafunta.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani