1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar China da Iran

January 16, 2006

Ga alamu China ba zata yarda a kakaba wa kasar Iran takunkumin karya tattalin arzikin kasa ba

A dai halin da ake ciki yanzu manazarta al’amuran siyasa a cibiyoyin bincike na kasar China suna dari-dari wajen tofa albarkacin bakinsu akan matsalar kasar Iran dake dada yin tsamari a diplomasiyyance. Jami’ai a wadannan cibiyoyi su kann kauce wa tambayoyin manema labarai, tare da ikirarin cewar da wuya su iya fadar wani abu akan matsalar, ko kuma su ce wai ba su da wata masaniya game da wannan lamari. To sai dai kuma wani kwararren masanin da ya ce ba ya so a ambaci sunansa ya bayyana imanin cewar fadar mulki ta Peking ba ta kaunar bayyana matsayinta akan wannan batu a gaban kwamitin sulhu na MDD. A sakamakon haka kasar China ke sauraro ta ga irin alkiblar da Rasha zata fuskanta. An dai saurara daga bakin farfesa Götz Neuneck daga cibiyar binciken manufofin zaman lafiya da tsaro dake birnin Hamburg yana mai bayanin cewar:

Kasashen China da Rasha ba sa kaunar ganin an samu gurbacewar yanayin dangantaka tsakaninsu da kasar Iran sakamakon yarjeniyoyin makamashi dake akwai tsakaninsu da kasar Iran. Wato dai hakan na nufi ne cewar ba bu wata daidaituwar ra’ayi tsakanin illahirin dawwamammun wakilan kwamitin sulhu na MDD akan wannan batu ko da yake kusan dukkansu sun hakikance cewar bai kamata kasar ta Iran ta mallaki makaman kare dangi ba.

Amma duk da haka akwai tababa a game da matsayin kasar China dangane da hana yaduwar fasahar sarrafa makaman kare dangin. A bangare guda an dade ana tuhumar kasar ta China da cinikin fasahar sarrafa makamai, abin da ya hada har da na kare dangi, a asurce. Sannan a daya bangaren kuma kasar ba zata iya daukar wasu tsauraran matakai na hana yaduwar fasahar sarrafa makaman na kare dangi ba ta la’akari da irin rawar da take so ta taka a kasashe masu tasowa da masu matsakaicin ci gaban masana’antu. Dangane da kasar rasha kuwa, kamar yadda farfesa Neuneck ya nunar, an lura da kusantar manufofi tsakaninta da Amurka a game da maganar hana yaduwar fasahar sarrafa makaman na kare dangi. Kuma wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya kasar Rasha tayi tayin tace ma’adaninta na Uranium a harabar kasar ta Rasha, amma ita China tayi watsi da wannan batu duk kuwa da cewar tana da cikakkiyar fasahar tace uranium din. Kasar ta China tana bakin kokarinta wajen ganin Iran ta shiga ana damawa da ita a kungiyoyi na yankuna, wadanda Chinar ke da angizo a cikinsu. Ta la’akari da haka mai yiwuwa kasar ta haye kujerar naki in har lamarin ya kai ga shawarar kakaba wa Iran takunkumin karya tattalin arzikin kasa a kwamitin sulhu na MDD.